Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Yawan wadanda COVID-19 ta harba ya haura mutum miliyan 35
2020-10-06 17:00:37        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce ya zuwa jiya Litinin, adadin wadanda suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19 a daukacin sassan duniya ya kai mutum 35,109,317, yayin da jimillar wadanda cutar ta hallaka ya karu zuwa mutum 1,035,341.

Har ila yau, ita ma jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, ta fitar da wasu alkaluma a jiyan, wadanda ke nuna cewa, ya zuwa jiya da yamma, da misali karfe uku da minti 23, a Amurka kadai cutar ta hallaka sama da mutum 210,000, cikin mutum 7,445,897 da aka tabbatar sun harbu da ita a kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China