Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su kawar da matakan dake tarnaki ga aiwatar da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta nahiyar
2020-10-05 17:20:45        cri
Hukumar kula da ayyukan Tarayyar Afrika AU, ta yi kira da a kawar da matakan dake tarnaki ga aiwatar da manyan burikan yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta nahiyar Afrika.

A cewar AU, duk da sanin mummunan tasirin da matakan ke yi, kawo yanzu, ba a samu nasara ta a zo a gani ba wajen magance su.

Yayin da ake tsananin bukatar kawar da wadancan abubuwa domin samun nasarar aiwatar da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci, a wannan makon, AU ta kaddamar da wani sabon gangami da zai bayyana tare da kawar da matakan.

A cewar AU, ana hasashen gangamin mai taken "Trade Easier Campaign" wato cinikayya cikin sauki, zai inganta amfani da dandalin tattara matakan dake yiwa cinikayya tarnaki na tarayyar, wanda ke zaman wata hanya ko dabara ta bada rahoton matakan da ba na haraji ba, dake yi wa cinikayya cikas.

Dabarar, wadda AU ta samar da hadin gwiwar dandalin raya harkokin cinikayya ta MDD (UNCTAD), za ta taimakawa kokarin saukaka cinikayya a nahiyar da rage tsadarsu, ta hanyar taimakawa 'yan kasuwa bada rahoton abubuwan dake kawo musu cikas da kuma taimaka musu wajen kawar da su da taimakon gwamnatoci.

A cewar wani rahoton hukumar UNCTAD, idan aka cire matakan masu tarnaki ga cinikayya, tattalin arzikin Afrika zai samu karuwar dala biliyan 20, adadin da ya haura dala biliyan 3.6 da za ta iya samu idan ta kawar da biyan haraji. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China