Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ce yana samun lafiya
2020-10-04 18:04:46        cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump, wanda a halin yanzu yake jinya a wani asibitin sojoji dake kasar samakaon kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19, ya sanar a ranar Asabar cewa, yana samun sauki sosai, ya kuma ce zai fuskanci hakikanin gwaji nan da wasu kwanaki masu zuwa.

Shugaban na Amurka ya ce, "Na zo nan wajen ne, saboda rashin lafiyar jikina. Amma yanzu ina samun sauki, ana yin aiki tukuru domin ganin na samu koshin lafiya," Trump ya bayyana hakan ne cikin wani kajeren sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na tweeter. "Ina tunanin zan warke nan bada jimawa ba."

Ya ce, "Ina duba yiwuwar kammala yakin neman zabe, kamar yadda aka fara da kuma kamar yadda muka saba yi," shugaban wanda ke neman wa'adin mulki na biyu ya bayyana hakan.

"Nan da wasu 'yan kwanaki masu zuwa, ina tsammanin za a yi hakikanin gwaji," in ji shi. "Don haka za mu ga me zai faru nan da wasu kwanaki masu zuwa a nan gaba."

Trump ya kara da cewa, mai dakinsa, Melania, wacce gwajin da aka yi mata ya nuna cewa ita ma ta kamu da cutar COVID-19 tana killace kanta a fadar White House, " kuma tana samun sauki sosai."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China