Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ba zata laminci duk wani nau'in cin zarafin yin lalata ba
2020-10-04 18:03:53        cri
A kwanan nan, hukumar lafiyar ta duniya WHO, ta ce zata cigaba da mayar da hankali kan zarge-zargen dake shafar aikata cin zarafi ta hanyar lalata da ake samu a yankunan dake fama da annobar Ebola a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, hukumar ta bayyana bacin ranta kan faruwar lamuran tare da yin alkawarin gudanar da zuzzurfan bincike kan lamarin.

Daraktan hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, a yayin da hukumar WHO ke gudanar da aiki a sassan duniya domin ceto rayuka a yankunan dake cikin matsanancin hali. Ya ce wadannan ayyukan cin amanar al'ummar da suke yi wa hidima tilas ne a yi tir dasu kuma ba za a taba lamintarsu ba. Duk wanda aka samu yana da hannu wajibi ne ya fuskanci hukunci mai tsanani wanda ya hada har da kora daga aiki.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China