Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar tsakanin gwamnatin Sudan da 'yan tawayen kasar
2020-10-04 18:03:02        cri
Kasar Masar ta yi marhabun da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyin 'yan tawayen kasar, kamar yadda gwamnatin Masar ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar, inda ta ce yarjejeniya ce mai cike da tarihi.

Makwabciyar kasar, wato Sudan ta kudu ce ta karbi bakuncin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar wanda aka gudanar a ranar Asabar a Juba, wanda ya samu halartar wakilai daga kasar Masar karkashin jagorancin firaiministan Masar, Mostafa Madbouly.

Sanarwa ta ce, kasar Masar ta kasance a matsayin shaida a bikin yarjejeniyar mai cike da tarihi.

Sanarwar ta kara da cewa, yarjejeniyar zaman lafiyar ta bude wani sabon shafi na cigaba a tarihin Sudan, inda kokarin bangarori daban daban na mutanen kasar da kungiyoyi 'yan tawayen kasar suka hada kai don yin aiki tare da nufin ciyar da kasar gaba da kuma samarwa kasar makoma mai haske.

A cewar sanarwar, kasar Masar ta jaddada aniyarta na yin dukkan kokarinta wajen taimakawa shirin wanzar da zaman lafiyar Sudan.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China