Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana gudanar da ayyukan hadin-gwiwar Sin da Afirka yadda ya kamata
2020-10-04 16:21:54        cri

Kwanan nan, an kammala aikin shimfida hanyar mota ta Kabudi dake jihar Malanje a kasar Angola, wadda kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin ginawa.

Tsawon hanyar Kabudi ya kai kilomita 63.5, wanda ya zama muhimmin bangare a cikin manyan hanyoyin mota dake Angola. Allah ya albarkaci yankin da shinkafa da kifaye, a sabili da haka, bayan da aka kammala aikin shimfida hanyar motar, zata taimaka sosai ga ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma.

Duk da cewa cutar COVID-19 tana ci gaba da bazuwa, kamfanonin kasar Sin dake Afirka basu dakatar da ayyukansu ba har ma suna yin bakin kokarinsu wajen gudanar da ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya". Rahotanni daga ma'aikatar harkokin wajen Sin sun ce, ana tafiyar da ayyukan hadin-gwiwar Sin da Afirka sama da 1100 yadda ya kamata, kuma har yanzu akwai dimbin ma'aikatan kasar Sin wadanda suke bakin aikinsu a kasashen Afirka da dama. Gwamnatin kasar Sin ta kuma tura ma'aikata sama da dubu 2 zuwa kasashen Afirka 20, domin farfado da ayyukansu. Daga watan Janairu zuwa Yunin bana, darajar kasuwancin da aka yi tsakanin Sin da Afirka ta zarce dala biliyan 80, kuma yawan kudin da Sin ta zubawa nahiyar Afirka ya karu da kaso 1.7 bisa dari, abun da ya shaida babban ci gaban hadin-gwiwar dake kasancewa tsakanin bangarorin biyu.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China