Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon salon tattalin azikin kasar Sin yana samar da sabon zarafin ci gaban kasar
2020-10-04 16:07:40        cri

Bisa sabon rahoton da cibiyar samar da bayanai ta kafar sadarwar Intanet ta kasar Sin ta bayar, zuwa karshen watan Yunin bana, adadin tashoshin samar da karfin sadarwar 5G da aka gina a kasar ya zarce dubu 400, kana zuwa karshen bana, wannan adadin zai wuce dubu 600. Karuwar tashoshin fasahar sadarwar 5G ya alamta cewa, ana kokarin inganta wasu sabbin muhimman ababen more rayuwar al'umma a kasar ta Sin.

Sabbin ababen more rayuwar al'umma na nufin ababen da suka samo asali daga bangaren kimiyya da fasaha, wadanda suka shafi sadarwa, wutar lantarki, zirga-zirga da yanar gizo da sauransu. Inganta irin wadannan ababen zai yi amfani sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a zamanin da muke ciki na bukatar da ake da shi na yawan amfani da fasahar sadarwar Intanet. Kana babban burin da aka sanya a gaba shi ne, kara sabuntawa gami da yin kirkire-kirkire ga wasu sana'o'i, ta yadda za'a kara samar da kuzari wajen habakar tattalin arzikin kasar.

Shekarar da muke ciki, shekara ce ta karshe na shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13. Nan da shekaru biyar dake tafe, kasar Sin za ta shiga wani sabon mataki na ci gaba, inda tattalin arzikinta zai ci gaba da bunkasa yadda ya kamata, al'amarin da ya bukaci a kara yin kirkire-kirkire. Raya sabon salon tattalin arziki, don kara taimakawa inganta sana'o'i da kawo sauye-sauye ga karfin tattalin arziki, har ma zai amfanawa farfado da ayyukan samar da kayayyaki a duk fadin duniya, abin da zai iya samar da sabbin damammaki ga tattalin arzikin duniya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China