Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Donald Trump zai yi jinya a asibitin sojoji tsawon wasu kwanaki masu zuwa
2020-10-03 16:55:22        cri
Fadar White House ta Amurka, ta ce shugaba Donald Trump, zai yi jinya a asibitin sojoji na kasar cikin wasu kwanaki masu zuwa, bayan gwaji ya nuna yana dauke da cutar COVID-19.

Cikin wata sanarwa, sakataren yada labaran fadar, Kayliegh McEnany, ya ce Donald Trump wanda bai nuna alamu masu tsanani ba, yana nan lafiya kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa.

Da sanyin safiyar jiya Juma'a ne Trump ya sanar da cewa, shi da mai dakinsa Melania, sun kamu da cutar COVID-19, jim kadan bayan ya tabbatar da cewa wata hadimarsa dake da kusanci da shi ta kamu da cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China