Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abotar Sin da Nijeriya ta har abada ce
2020-10-02 17:06:01        cri

Tsohon Daraktan cibiyar nazarin wanzar da zaman lafiya da sulhu ta Nijeriya, Farfesa Joseph Golwa, ya wallafa wani sharhi mai taken " Murnar cika shekaru 50 da abotar Nijeriya da Sin" a ranar 30 ga watan Satumba, cikin jaridar The Nation ta kasar.

Sharhin ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya a shekarar 1971, Nijeriya da Sin sun hada kai bisa fahimta da girmama juna, kuma dangantakarsu ta rayu cikin aminci. Ya ce Nijeriya da Sin na goyon bayan juna dangane da batutuwan da suka shafi kasa da kasa, kamar muradun ci gaba masu dorewa da sauyin yanayi. Kuma kasar Sin ta zuba jari sosai a Nijeryia a bangaren sufurin jiragen kasa da shimfida tituna da tashoshin ruwa da filayen jirgin sama da sauran ayyukan more rayuwa, kuma yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu na ta habaka.

Ya ce a baya-bayan nan, tsarin taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da shawarar Ziri daya da hanya daya da sauran wasu manufofi, sun samu nasara sosai ta fuskar inganta tuntubar juna kan manufofi da tafiyar da cinikayya da dunkulewar harkokin kudi da samun mu'amalar al'umma. Har ila yau, ya ce Nijeriya ta zama daya daga cikin manyan abokan cinikayyar Sin a nahiyar Afirka, sannan wuri na biyu mafi girma da Sin take kai kayayyakinta, haka kuma ita ce kasa ta 6 mafi samar mata da danyen man fetur, kuma wuri na biyu da Sin din tafi zubawa jari a nahiyar Afrika.

A cewar sharhin, bayan barkewar annobar COVID-19, Nijeriya da Sin sun marawa juna baya, inda suka hada hannu wajen yaki da ita. Ya ce kasar Sin ta gaggauta samar da adadi mai yawa na kayayyakin kiwon lafiya ga Nijeriya, sannan ta gabatar da matakanta na yaki da annobar.

Haka zalika, Nijeriya da Sin 'yan uwa ne kuma abokan hulda. Don haka, wadanda ke son lalata muhimmiyar huldar abota da suka kulla cikin shekaru 50 da suka gabata, ba za su yi nasara ba.

An yi ammana cewa, bisa hadin gwiwar kasashen biyu, 'yan uwantakarsu za ta kasance ta har abada. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China