Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Trump da mai dakinsa sun kamu da cutar COVID-19
2020-10-02 16:46:55        cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya bayyana da sanyin safiyar yau Juma'a cewa, shi da mai dakinsa Melania, sun kamu da cutar COVID-19, bayan wata hadimarsa ta kamu da cutar.

Ya wallafa a shafinsa na tweeter cewa, za su fara killace kansu da neman samun lafiya nan take.

Sanarwar ta zo ne sa'o'i bayan shugaban ya tabbatar da wata babbar hadimar fadar white House, Hope Hicks, ta kamu da cutar.

Cikin wannan makon, Hope Hicks, wadda ke da kusanci da shugaban, ta yi tafiye-tafiye tare da shi, ciki har da tafiyar da suka yi cikin jirgin shugaban kasar zuwa yakin neman zabe a Minnesota a ranar Laraba, da kuma tafiyar da suka yi Cleveland, domin halartar muhawarar 'yan takarar shugabancin kasar a zaben bana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China