Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bachelet: Ofishin kare hakkin bil-Adama na MDD na ci gaba da karbar rahotanni kan yadda ake nunawa 'yan asalin Afirka wariyar launin fata
2020-10-02 16:21:05        cri
A jiya ne, babbar kwamishiniyar hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD, Michelle Bachelet, ta gabatarwa taron hukumar kare hakkin bil-Adama na MDD karo na 45 dake gudana a halin yanzu, wasu shaidu, game da wariyar launin fata. Tana mai cewa, ofishinta na ci gaba da karbar rahotanni kan yadda 'yan sanda ke cin zarafin 'yan asalin Afirka.

Ta kuma shaidawa hukumar ayyukan da ta gudanar, game da yadda ake gallazawa 'yan asalin Afirka a sassan duniya, wadanda suka hada da nuna musu rashin daidaito da wariya, yayin tashin hankali, da wadanda 'yan sanda ke nunawa.

A farkon watan Yunin wannan shekara, bayan mutuwar Ba-Amurken nan mai suna George Floyd a Minneapolis da wasu bakaken fata 'yan asalin Afirka, zaman hukumar karo na 44, ya yanke kuduri, inda da kakkausar murya ya yi Allah wadai da yadda hukumomin tsaro ke ci gaba da nunawa bakaken fata 'yan asalin Afirka wariyar launin fata da cin zarafi.

Shi ma shugaban rukunin kungiyar gwamnatoci dake kokarin ganin an aiwatar da yarjejeniya da shirin da aka amince a birnin Durban Refiloe Litjobo, ya bayyana yayin zaman na jiya cewa, annobar COVID-19 da ake fama da ita a halin yanzu, musamman ta shafi wasu rukunonin jama'a da tun tuni suke fuskanta wariya, ciki har da 'yan asalin Afirka.

A saboda haka ne, masu zanga-zanga a sassa daban-daban na duniya, dake goyon bayan Floyd, sun nuna cewa, kasashen duniya sun damu da matsalar nuna wariyar launin fata dake faruwa.

A muhawarar da aka tabka kan wannan jigo, wasu masu jawabi, sun yi Allah wadai da yadda kasashen yamma suka siyasantar da batun muna wariyar launin fata. Yayin da wasu kuma suka yi kira ga kasashen duniya, da su magance yadda ake take hakkin 'yan asalin kasa, abin da suke ganin a matsayin wani salo na nuna wariya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China