Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Buhari ya taya Xi murnar cika shekaru 71da kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin
2020-10-01 15:59:32        cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya aikawa takwaransa na kasar Sin Xi Jinping wasika, inda a ciki ya taya shi murnar cika shekaru 71 da kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin da kuma ranar kafuwar kasa.

Buhari ya ce, yana farin ciki cewa, dangantakar abokantaka tsakanin Najeriya da Jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta ci gaba da karfafa. Kana duk da cewa, annobar COVID-19 ta kawo illa ga tattalin arzikin duniya, amma kasashen biyu sun kasance masu hakuri da taimakawa juna.

Shugaba Buhari ya kuma yabawa gwamnatin kasar Sin, kan yadda take taimakawa wajen farfado da kayayyakin more rayuwa a Najeriya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China