Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe maso tasowa sun soke batutuwan kare hakkin bil-Adama na kasar Amurka da sauran kasashen Yamma
2020-09-29 20:33:05        cri
A yayin taron hukumar kare bil-Adama ta MDD karo 45 da aka gudanar, kasashe masu tasowa, sun soki kasar Amurka da kungiyar tarayyar Turai da kasashen Jamus, da Finland, da Sweden da Noway, kan yadda suke tafiyar da batutuwan da suka shafi kare hakkin bil-Adama.

A jawabinsa, wakilin kasar Venezuela, ya yi nuni da cewa, gwamnatin Amurka ta kasa yakar annobar COVID-19, kuma yanzu haka Amurka ce ke kan gaba wajen yawan mutanen da cutar ta halaka a duniya. Haka kuma kasar Amurka ba kawai ta yi watsi da hakkokin jama'arta ba, har ma ta kakabawa wasu kasashe takunkumi bisa kashin kanta, lamarin da ya kawo cikas ga kokarin kasashen da abin da shafa na yaki da annobar.

Shi ma wakilin kasar Masar, ya bayyana cewa, 'yan majalisar dokokin kasar Finland, sun sha bayyana kalaman nuna kiyayya da tsana kan 'yan asalin Afirka da musulmai. Baya ga yadda ake cin zarafin musalumi a kasar Sweden.

Wakilin kasar Sin ya yi nuni da cewa, matsalar kare hakkin bil-Adam a Burtaniya da Faransa da Jamus, da Jamhuriyar Czech da sauran kasashen Turai da Australia na kara tsananta, ana kuma kara samun matsalar nuna kyama da wariyar launin fata. Abin takaici, wadannan kasashe ba sa jin kunya, su kalli matsalarsu, ko su ambaci batutuwan da suka shafi hakkin bil-Adama a kasashe kawayensu. Maimakon haka, sai su tilastawa wasu kasashe abin da za su yi, kuma makircinsu game da manufofin da suka shafi hakkin bil-Adama ya bayyana.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China