Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta lashi takobin ci gaba da taimakawa bangaren ilimi a Sudan ta kudu
2020-09-29 11:03:31        cri

 

Gwamnatin kasar Sin ta lashi takobin ci gaba da samar da taimakon kwararru da na kayayyaki ga Sudan ta kudu, domin taimakawa kasar dake gabashin Afrika raya bangarenta na ilimi.

Jakadan Sin a Afrika ta kudu Hua Ning, ya ce sun yi ammana yara su ne manyan gobe a kowacce kasa, don haka komai rintsi, akwai bukatar ci gaba da bada ilimi ga dukkan yara.

Ya kara da cewa, Sin za ta zuba kimanin dala miliyan 20 a mataki na biyu na hadin gwiwarta da kasar a bangaren ilimi, sannan Sin na kuma duba yuwuwar kara bada taimako kan shirin sake bude makarantu a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China