Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kalla 'yan gudun hijira dubu 1 ne suka koma gidajensu a garin Baga
2020-09-28 19:47:49        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla 'yan gudun hijira dubu 1 suka koma gidajensu a garin Baga na jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar, bayan da mayakan Boko haram suka tarwatsa su daga muhallansu watannin da suka gabata.

Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta Litinin din nan, ta ruwaito gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum,wanda ya dawo birnin Maiduguri bayan shade kwanaki biyu a garin na Baga, yana kira ga 'yan gudun hijiar da suka koma, da su kasance masu bin doka, kana su hada kai da hukuomin tsaro, don tabbatar da doka da oda.

Bayanai na cewa, an baiwa duk wanda ya koma naira dubu 10, a matsayin kudin rage radadi. Sannan kowa ne magidanci ya samu buhun shinkafa daya, na masara daya, da buhun wake daya da kuma lita uku na man girki.

A ranar Jumma'a ne dai, mayakan Boko Haram suka yiwa ayarin jami'an gwamnati kwanton bauna, yayin da suke kan hanyar zuwa garin na Baga, don karbar 'yan gudun hijirar da suka koma gidajensu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China