Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya yayi Allah wadai da harin da aka kaddamar a arewa maso gabashin kasar
2020-09-27 20:47:55        cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yayi Allah wadai da babbar murya kan harin kwanton bauna da aka kaddamar a ranar Juma'a kan ayarin jami'an gwamnatin jahar Borno, dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yau Lahadi, shugaba Buhari, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da mutanen jahar, da gwamnatin jahar, da ma alummar Najeriya, kana yayi fatan samun sauki cikin hanzari ga mutanen da suka samu raunuka sanadiyyar harin.

Shugaban Najeriyar ya bayyana harin da cewa wani yunkuri ne na dakile aniyar shirin da aka jima ana yi na kokarin sake mayar da 'yan gudun hijirar zuwa yankunansu, inda ya bukaci jami'an tsaro, da hukumomin tattara bayanan sirri, su kara azama domin bankado mutanen dake da hannu wajen yin zakon kasan, sannan ya bukaci a gaggauta tsabtacce titunan motan yankunan, da kuma kara yin hadin gwiwa da al'ummomin yankunan domin gyara garuruwan gabanin komawar mutanen da rikicin ya tilastawa barin gidajensu.

Ya zuwa ranar Lahadin nan, rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar harin kwanton baunar na ranar Juma'a wanda mayaka 'yan ta'addan Boko Haram suka kaddamar kan ayarin tawagar jami'an gwamnatin jahar Borno ya kai 18.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China