Sin ta tura tawagar jami'an lafiya don tallafawa Lesotho da Angola yakar COVID-19
2020-09-27 17:17:52 cri
Gwamnatin kasar Sin ta tura tawagar kwararrun masanan kiwon lafiya zuwa kasashen Lesotho da Angola domin taimakawa kasashen biyu wajen yakar annobar COVID-19, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya sanar da hakan a yau Lahadi.
Wang yace, da sanyin safiyar yau Lahadi, tawagar ta tashi zuwa kasashen biyu na nahiyar Afrika.(Ahmad)