Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin ya mayar da martani kan zargin da Burtaniya ta yiwa kasarsa
2020-09-26 20:28:32        cri

A ranar 25 ga wata, jami'in diflomasiyyar kasar Burtaniya ya zargi kasar Sin kan batutuwan da suka shafi yankin Hong Kong da jihar Xinjiang na kasar Sin, yayin taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD, inda ya gabatar da wasu labarai na jabu, domin bata sunan kasar Sin, lamarin da ya nuna bambancin ra'ayi da rashin saninsa game da harkokin Sin.

Sai dai da yake mayar da martani kan furucin da wannan jami'i ya yi, kakakin tawagar zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD a birnin Geneva, Liu Yuyin ya bayyana cewa, batutuwan dake shafar yankin Hong Kong da jihar Xinjiang ba batutuwa ne na hakkin dan Adam ba, sai dai batutuwa ne dake shafar yadda kasar Sin take kare 'yancin kanta da zaman lafiyar kasa da dunkulewar kasa baki daya.

Ya ce, jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ta yi fama da barazanar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi mai tsanani, kuma al'ummar jihar sun fuskanci matsalolin take musu hakkokinsu na rayuwa da kiwon lafiya da kuma ci gaba. Yana mai cewa gwamnatin jihar, ta yi kokarin shawo kan matsalar, kana tana da karfin kare al'ummarta, ta yadda aka shimfida zaman lafiya a jihar Xinjiang, tare da tabbatar da jin dadin zaman al'ummominta.

Tun daga shekarar 2018, ya zuwa yanzu, jami'an diflomasiyya, da jami'an kungiyoyin kasa da kasa, da 'yan jaridu da masanan addinai da suka zo daga kasashe sama da 90 sun taba kai ziyara jihar Xinjiang, inda suka ganewa idanunsu bunkasuwar jihar Xinjiang, da yadda al'ummomin jihar suke jin dadin zaman rayuwarsu.

Wasu yammacin kasashen duniya da 'yan siyasarsu sun yada labarai na jabu masu dimbin yawa game da batun jihar Xinjiang domin bata sunan kasar Sin, da bata ran al'ummomin jihar Xinjiang, wanda abu ne da kasar Sin ba za ta yarda da shi ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China