Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasan Amurka masu son karya ne ke haifar da barazana ga aikin kare muhallin duniya
2020-09-25 21:49:44        cri

Kwanan baya, yayin taron MDD, shugaban kasar Amurka ya bata sunan kasar Sin ta fuskar kare muhallin duniya, har ma ya nuna alfaharinsa game da janye jiki daga yarjejeniyar Paris, inda ya yi tsokaci da cewa, kasar Amurka ita ce mai ba da babbar gudummawa wajen kare muhallin duniya.

Wannan karya da ya yi, ta nuna rashin tabbacinsa game da batun janye jiki daga yarjejeniyar Paris, lamarin da ya nuna cewa, wadannan 'yan siyasan kasar Amurka, su ne masu kawo barazana ga aikin kare muhallin duniya.

Sau da dama, kasar Amurka na neman bata sunan kasar Sin a tarukan kasa da kasa, domin matsa wa kasar Sin lamba, kuma, ta zargi kasar Sin game da batun kare muhalli, domin boye laifinta na bata hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa. Amma, duk da hakan, ba za a manta da gaskiyar wannan batu ba.

Kasar Sin tana iya nuna wa kasa da kasa sakamakon da ta cimma a fannin kare muhalli bisa ayyukan da ta yi. Kaza lika kasar Sin da al'ummunta sun cimma ra'ayi daya kan manufar neman bunkasuwa mai taken "koguna da tsaunuka masu tsabta su ne arziki". A shekarar 2018, adadin iska mai gurbata muhalli da kasar Sin ta fitar ta ragu da kaso 45.8%, idan aka kwatanta da na shekarar 2005. Kuma, ya zuwa karshen shekarar 2019, adadin sharar da aka gyara a biranen kasar Sin domin kada su gurbata muhalli, ta kai kaso 99% na dukkanin sharar da aka zubar. Yanzu haka, muhalli a kasar Sin yana ci gaba da samun kyautatuwa, lamarin da ya sa, al'ummomin kasar ke jin dadin zaman rayuwarsu, yayin da suke kuma samun amincewar kasa da kasa. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China