Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nature: Ya kamata kasa da kasa su saurari yadda kasar Sin ke kiyaye nau'o'in halittu a duniya
2020-09-25 14:01:25        cri
Mujallar Nature a ranar 23 ga wata ta wallafa wani sharhi, inda take ganin cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye nau'o'in halittu daban daban a duniya, kuma masana ilmin kimiyya na kasar Sin suna da fasahohin da suka cancanta kasa da kasa su koya.

Sharhin ya ruwaito takardar da sakatariyar yarjejeniyar kiyaye nau'o'in halittu ta MDD ta fitar a kwanan baya dangane da hasashen nau'o'in halittu na duniya, inda ya yi nuni da cewa, daga cikin burika 20 da ake sa ran za a cimma a shekarar 2020 a fannin kiyaye nau'o'in halittu da muhallinsu, guda 6 kacal aka yi nasarar cimmawa, sauran duk an gaza. Wani nazarin da aka gudanar a bara dangane da nau'o'in halittu ya shaida cewa, kimanin tsirrai da dabbobi miliyan guda suna bakin bacewa daga doron kasa.

Sharhin ya kara da cewa, kasar Sin ta shafe gomman shekaru tana nazarin hanyoyin daidaita matsalar da ke tsakanin bunkasuwar tattalin arziki da kiyaye nau'o'in halittu, wadda ta taimaka ga kiyaye nau'o'in halittu a duniya baki daya. Fasahohin masanan kasar Sin suna iya samar da muhimmiyar dama ga sauran kasashen duniya wajen kiyaye nau'o'in halittu da ma muhallinsu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China