Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya bukaci a dauki matakan daidaita matsalolin siyasa da tattalin arziki a Lebanon
2020-09-24 12:27:45        cri

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya ce, a ranar 4 ga watan Ogasta ne aka samu mummunar fashewa a tashar ruwan birnin Beirut, lamarin da ya haifar da mummunan tashin hankali ga mutanen Lebanon. Sakamakon fashewar, da annobar COVID-19, da tashe tashen hankula a shiyyoyin da kasar ke ciki sun haifar da manyan kalubaloli ga yanayin tattalin arziki da zaman rayuwar al'ummar kasar ta Lebanon.

A tsokacin da yayi, a taron ministocin hukumomin tallafin kasa da kasa ga kasar Lebanon wanda aka gudanar ta kafar bidiyo, Zhang ya bukaci a samar da wani ingantaccen yanayi domin daidaita al'amurran siyasar kasar Lebanon.

Zhang ya ce, kasar Sin a koda yaushe tana goyon bayan Lebanon a kokarin tabbatar da ikon mulkin kasa da tsaron kasa, gami da bunkasa tattalin arziki da zaman rayuwar al'ummar kasa. Kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da hukumomin tallafin kasa da kasa domin bayar da gudunmawar sake gina Lebanon, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da kuma ci gaban kasa a Lebanon.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China