Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 23 sun mutu a fashewar tankar mai a tsakiyar Najeriya
2020-09-24 12:20:14        cri

A kalla mutane 23 ne suka mutu, wadanda suka had da dalibai, sakamakon fashewar wata tankar mai a jahar Kogi, dake shiyyar tsakiyar Najeriya, jami'an 'yan sandan wurin sun tabbatar faruwar lamarin.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba a yankin Felele dake jahar Kogi, a babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja yayin da birkin tankar man ya samu matsala.

A cewar jami'an, tankar man ta fadi a kan titin mota inda nan take ta yi bindiga, lamarin da ya shafi baburan hawa biyu, da motoci biyar, da kuma baburan keke nafef guda uku.

Dukkan mutanen dake cikin ababen hawan har ma da masu wucewa da kusa da wajen wutar ta kona su.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China