Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen babban taron MDD
2020-09-23 13:48:23        cri


Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen muhawarar babban taron MDD karo na 75, inda ya nanata cewa, ganin yadda annobar COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a duniya, ya dace kasa da kasa su maida moriya gami da rayuwar mutane a gaban kome, da karfafa zama tsintsiya madaurinki daya. Xi ya kuma jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da bin tafarkin neman bunkasuwa cikin lumana, da bude kofarta ga kasashen ketare, tare kuma da kara bada gudummawa ga kiyaye doka da oda da ci gaban duniya baki daya.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya ce, a halin yanzu al'ummun kasashe daban-daban na fama da cutar COVID-19, inda suke taimakawa da kula da nuna kauna ga juna gami da nuna jarunta sosai wajen yaki da wannan annoba. Game da yadda ake iya dakile cutar, shugaba Xi ya bayar da wasu muhimman shawarwari guda hudu:

"Ya kamata mu maida muradun jama'a gami da rayuwarsu a gaba da kome, da yin duk wani kokari na kula da wadanda suka kamu da cutar, domin taka birki ga yaduwar cutar. Sa'annan ya zama dole mu fadada hadin-gwiwa da zama tsintsiya madaurinki daya, da kara muhimmiyar rawar da kungiyar WHO take takawa wajen jagorancin ayyukan yaki da cutar. Bai kamata a saka batun siyasa ko bata sunan wata kasa a yayin da ake dakile yaduwar cutar ba. Har wa yau, ya dace a tsara kyawawan manufofin farfadowa bayan cutar daga dukkanin fannoni, da kokarin farfado da harkokin kasuwanci da kasuwanni da ayyukan kere-kere da kuma karatu, da kara samar da guraban ayyukan yi, da sake raya tattalin arziki. Bugu da kari, ya kamata a kara kulawa da kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, da daukar wasu kwararan matakan da suka shafi soke basussuka, da samar da tallafi, domin taimaka musu haye wahalhalun da suke fuskanta."

Shugaba Xi ya nuna cewa, kasarsa na himmatuwa wajen ganin bayan yaduwar cutar a duk fadin duniya, za kuma ta ci gaba da bayyanawa sauran kasashe fasahohi gami da dabarunta na yaki da cutar, da samar da tallafi da goyon-baya ga duk wata kasa da take da bukata, gami da kara shiga ayyukan binciken asalin kwayar cutar da hanyoyin yaduwarta. Kawo yanzu, Sin ta samu babban ci gaba wajen gwajin allurar rigakafin cutar COVID-19, kuma da zarar an fara amfani da ita, za'a fara baiwa kasashe masu tasowa ne.

Shugaba Xi ya kara da cewa, akwai wasu muhimman darussa hudu da muka koya daga aikin yaki da cutar. Na farko, akwai alaka ta kut da kut tsakanin kasa da kasa:

"Bai dace ba wata kasa ta samu riba ko moriya daga wahalhalun da wasu kasashe suke fuskanta, ko kuma samun kwanciyar hankali daga tashin hankali a sauran wasu kasashe. Wato abun da ya taba hanci, ido ma ruwa yake. Ya dace a fahimci cewa, kowa na da alaka da wani, bai kamata a raba su ba."

Na biyu shi ne, dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya, abu ne da bai kamata a kyale shi ba. Na uku shi ne, akwai bukatar dan Adam ya maida hankali kan kiyaye muhallin halittu, wato bai dace ba a nemi ci gaba kawai amma ba tare da la'akari da muhimmancin kiyaye muhallin halittu ba. Na hudu wato na karshe shi ne, akwai bukatar yin garambawul da ci gaba da kyautata tsarin tafiyar da harkokin duniya. Wato annobar COVID-19 ba jarabta kwarewar kasa da kasa wajen tafiyar da harkokin mulki kawai take yi ba, har ma tana jarabta tsarin tafiyar da harkokin duniya baki daya:

"Ya kamata a martaba ra'ayin cudanyar bangarori daban-daban, da kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD. Har wa yau, ya zama dole kasa da kasa su kara yin shawarwari da more damammaki tare a yayin da ake tafiyar da harkokin duniya, da shimfida adalci a fannonin da suka shafi kare hakki da samar da zarafi da kuma kafa ka'idoji, ta yadda za'a samu ci gaba cikin lumana da karfafa hadin-gwiwa da cin moriyar juna tare."

A karshen jawabin, shugaba Xi ya jaddada cewa:

"Ya kamata mu sauke nauyin da aka danka mana, da yin zabin da ya dace wanda ba za mu yi da-na-sani ga jama'a da tarihi ba. Ya dace mu karfafa hadin-gwiwa tsakaninmu, da tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa, da shimfida adalci da tsarin demokuradiyya da neman samun 'yanci, domin kafa wata sabuwar dangantakar kasa da kasa, da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China