Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun UNICEF ya yi kira da a dauki matakan kariya yayin sake bude makarantu a Afirka
2020-09-23 10:45:10        cri

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya yi kira ga gwamnatocin kasashe gabashi da kudancin Afirka, da su gaggauta tare da sake bude makarantu, ba tare da wata matsala ba, a yayin da ake ci gaba da kara tafba hasara, biyo bayan rufe makarantun a sassan shiyyar.

A cewar asusun na UNICEF, kasashe 13 cikin kasashe 21 dake gabashi da kudancin Afirka ne, kawai suka bude makarantunsu, yayin da aka kara samun kasashe 4 da suka sanya ranakun sake bude nasu makarantun.

Da yake Karin haske kan wannan batu, darektan shiyya na asusun UNICEF mai kula da gabashin Afirka Mohamed Malick Fall, ya ce nahiyar ta fuskanci koma bayan shirin koyarwa, da karuwar tashin hankali, da bautar da yara, da tilastawa yara mata auren wuri, da yadda kananan yara ke daukar ciki, da karancin abinci mai gina jiki. Wannan ya sanya wata zuriyar yara cikin hadari, kuma wannan shi ne lokaci mafi sarkakiya a tarihin nahiyar.

A cewar UNICEF, akwai yiwuwar za a bude makarantun ba tare da wata matsala ba a farkon watan Oktoban dake tafe, kuma hakan zai baiwa masana cikakken zangon karatu, da ma rage hasarar da aka tabfa a fannin koyo.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China