Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ya kamata a ingiza farfado da tattalin arziki maras gurbata muhalli bayan COVID-19
2020-09-23 10:32:36        cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, bai kamata bil Adama su yi biris da kashedin da ake yi musu daga indallahi ba, sannan su ci gaba da bin tsohuwar hanyar neman kudi ba tare da zuba jari, da neman bunkasuwa ba tare da kiyaye muhalli ba, har ma da amfani da muhalli ba tare da inganta shi ba.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, a jawabin da ya gabatar a babbar muhawara ta babban taron MDD karo na 75 da aka shirya jiya Talata.

Xi ya jaddada cewa, yarjejeniyar Paris wadda ta mai da hankali kan tinkarar matsalar sauyin yanayi, ta zayyana alkiblar da duniya ke bi ta samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, kana wani mataki mai tushe da ake dauka don kiyaye duniya da muke ciki, a don haka, dole ne kasashe daban-daban su dauki matakai da suka dace. Ban da wannan kuma, ya kamata kasashen duniya su bullo da sabon tunani na samun bunkasuwa wato yin kirkire-kirkire da sulhuntawa da kiyaye muhalli da bude kofa da ma more ci gaba tsakaninsu, ta yadda za a yi amfani da zarafi mai kyau na juyin juya halin masana'antu da kimiya da fasaha a sabon zagaye, don ingiza farfadowar tattalin arziki maras gurbata muhalli bayan annobar cutar COVID-19. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China