Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kungiyar AU ya yi kira da a kara yawan wakilcin kasashen Afirka a MDD
2020-09-23 09:54:59        cri

Shugaban kungiyar tarayyar Afirka, kana shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kira da a kara yawan kasashen nahiyar Afirka a cikin kwamitin sulhu na MDD (UNSC).

Ramaphosa ya yi wannan kira ne jiya Talata, yayin da yake jawabi a babban taron MDD karo 75 da ya gudana da kafar bidiyo. Ya yi nuni da cewa, yiwa kwamitin sulhun MDDr gyaran fuska, zai taimaka wajen warware tashe-tashen hankulan dake faruwa a sassan duniya.

Shugaba Ramaphosa ya ce, kasashen dake cikin kwamitin sulhun a halin yanzu, bai yi daidai da yadda muke rayuwa a duniya ba. A don haka, ya nanata cewa, "a yayin da MDDr ke bikin cika shekaru 75 da kafuwa, muna nanata kiranmu na kara wakilcin kasashen Afirka a kwamitin sulhun majalisar, kuma ya kamata a gagguta gabatar da wannan batu a taron kungiyoyin shiyyar. Ya kuma kira da a yafewa kasashen nahiyar kudaden ruwa na basussukan da ya kamata su biya, a daidai gabar da kasashen nahiyar ke murmurewa daga annobar COVID-19.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China