Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO da UNICEF sun kaddamar da shirin riga kafin shan-Inna a Somaliya
2020-09-22 10:50:59        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF), sun kaddamar da shirin yiwa yara kimanin miliyan 1.65 'yan kasa da shekaru 5 alluran riga kafin cutar shan-Inna a yankunan kudanci da tsakiyar kasar Somaliya.

A don haka, hukumomin biyu sun shawarci ma'aikatan lafiya da masu reno, da su kiyaye matakan lafiya da tsaro game da COVID-19 a yayin shirin riga kafin na kwanaki hudu.

Da yake Karin haske kan shirin riga kafin, wakilin asusun UNICEF a kasar Somaliya, Werner Schultink, ya bayyana cewa, shirin zai taimaka wajen kara dakile bazuwar annoba, zai kuma kare yara daga kamuwa da cututtukan dake halaka yara, ta yadda za su rayu kamar kowa.

Shi ma wakilin WHO a kasar ta Somaliya, Mamunur Rahman Malik, ya bayyana cewa, hanya daya tilo ta kawo karshen irin wannan barkewar cututtukan da za a iya yakarsu ta riga kafi, ciki har da shan-Inna, shi ne yiwa ko wane yaro riga kafi a kan lokaci, walau ta hanyar shirye-shirye da aka saba ko irin wannan rigakafi na gama gari.

Shirin riga kafin dai, na zuwa ne, a kokarin da ake yi na hana yaduwar cutar Shan-Inna da ta barke a yankunan kudanci da tsakiyar kasar Somaliya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China