Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana ketare sun yaba shawarar shugaba Xi ta martaba alakar bangarori daban-daban da gina makoma ta bai daya
2020-09-22 10:33:09        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, wajibi ne MDD ta kasance mai nuna adalci, da martaba doka, da bunkasa alakar kasancewar bangarori daban-daban, da mayar da hankali kan matakan da suka dace a dauka bayan ganin bayan annobar COVID-19.

Xi, ya bayyana haka ne, a jawabin da ya gabatar yayin taron manyan jami'an MDD da aka shirya ta kafar bidiyo, don murnar cikar MDDr shekaru 75 da kafuwa. Ya kuma nanata kudirin kasar Sin na kasancewar bangarori daban-daban, da yin gyare-gyare da bunkasa tsarin tafiyar da harkokin duniya, tare da alkawarin gina al'umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama.

Jawabin na shugaba Xi ya samu yabo daga masana na ketare, inda suka bukaci kasashen duniya da su kara hada kai, don daukar matakan da suka dace na tunkarar barazana da kalubalen da duniya ke fuskanta.

Babban sakataren MDD, Antonio Guterres da babban darektan hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya, duk sun bayyana cewa, kalaman shugaba Xi game da kudirin kasarsa na nacewa ga kasancewar bangarori daban-daban kan harkokin kasa da kasa, wata alama ce a fili dake nuna babbar rawar da tsarin MDD yake takawa, na kasancewa tare da goyon bayan kasashe mambobin majalisar, a wannan lokaci da duniya ke fama da wannan annoba.

Shi ma darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju, ya bayyana cewa, kasar Sin ta fito da wata taswira a zahiri dake bayyana bukatar gina al'umma ta bai daya, ta hanyar amfani da shawarar nan ta "Ziri daya da hanya daya", don kafa tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa ba tare da wata rufa-rufa ba, wanda kuma zai kunshi kowa da kowa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China