Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkalin Amurka ya daina takunkumin da gwamnatin kasar ta sanyawa manhajar WeChat
2020-09-21 15:44:43        cri

Kafar yada labarai ta Reuters ta ba da labarai jiya Lahadi cewa, wani alkalin kotun jihar California ya gabatar da wani umurnin dakatar da takunkumin da ma'aikatar kasuwancin kasar ta sanyawa manhajar Wechat dake ketare a ran 18 ga wata, don hana kamfanin Apple da Google su kawar da Wechat daga kantinsu na wayar salula tun daga ran 20 ga wata.

Alkalin kotun jihar California Laurel Beeler ya ce, zargin da gwamnatin Donald Trump ta yiwa WeChat wai manhajar tana kawo barazana ga tsaron kasar, babu shaidu, kuma matakin ba zai yi amfani wajen tabbatar da muradun kasar ba ko kadan. Ya zuwa yanzu, ma'aikatar kasuwancin Amurka ba ta maida martani ga shawarar da kotun ta yanke ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China