2020-09-21 11:47:42 cri |
Tun daga watan Oktoban shekarar 2007, kasar Sin ta fara tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa yankin Darfur na kasar Sudan, ya zuwa karshen watan Agustan bana, ta riga ta aika sojojin injiniya zuwa yankin har sau 16.
Sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura yankin Durfur na kasar Sudan a karshen watan Agustan bana, sun bayyana cewa, za su sauke nauyin kiyaye zaman lafiya na sojojin kasar Sin ta hanyar daukar hakikanan matakai.
Yankin Darfur dake yammacin kasar Sudan, a baya ya yi fama da matsalar tashin kwanciyar hankalin masu adawa da gwamnatin kasar, sakamakon hargitsin da ya faru tsakanin kabilun kasar a shekarar 2003, ya zuwa watan Yulin shekarar 2007, kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani kudurin cewa, za a tura rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa yankin, a watan Agustan bana ne, kasar Sin ta tura rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta 16 zuwa yankin, inda ta kasance rundunar sojoji daya kacal wadda ke gudanar da aikin injiniya dake karkashin jagorancin tawagar jami'an tsaron da MDD da kungiyar tarayyar Afirka wato AU suka tura zuwa yankin cikin hadin gwiwa.
Shugaban rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta 16 ta kasar Sin Xiao Wei ya yi mana bayani cewa, gaba daya adadin sojojin rundunar ya kai 225, an jibge su a sansanoni uku wato el-Fashir, Glo, da kuma Natiti, muhimman ayyukansu sun hada da gyara hanyoyi da filayen aiki da gidaje da filayen saukar jiragen sama da gina gine-ginen aikin soji da sauransu, yana mai cewa, "Yanayin aikin da muke yi a wannan karo yana da sarkakiya, da farko, wuraren aikinmu suna da nisa, wato sansaninmu dake el-Fashir yana da nisan kilomita 153 daga sansanin Glo, sai kuma nisan kilomita kusan 180 daga sansanin Natiti, yana da wahala a tabbatar da bukatun rayuwarmu, kana sansanonin Glo da Natiti suna kan tuddai ne, yayin da ake fama da dakaru masu adawa da gwamnatin kasar da dama, hargitsi ya kan barke, har ma ya kan kawo mana barazana."
Ban da haka, annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa a yankin, Xiao Wei ya bayyana cewa, kafin tashinsu daga nan kasar Sin, sun samu horo har sau uku, inda suka koyi yadda za su dakile annobar, bayan da suka isa yankin Darfur na Sudan, sun sanar da sauyin yanayin yaduwar cutar a kan lokaci ta hanyar lika takardar sanarwa ko samar da bayanai ta manhajar WeChat, ta yadda za su yi nasarar rigakafin yaduwar annobar a sansanoninsu, Xiao Wei ya ce, "Hakika muna alfahari saboda muna gudanar da aikin kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa a yankin Darfur na kasar Sudan, yawancin sojojinmu sun taba shiga gasar aikin sojin kasa da kasa, da atisayen aikin ceton kasa da kasa da kuma atisayen aikin sojin tsakanin kasa da kasa, wasu kuma wannan shi ne aikin kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa karo na biyu ko uku da suka shiga."
Xiao Wei ya kara da cewa, daya daga cikinsu, wato Zhang Wei ya gudanar da aikin kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa karo na uku, a don haka ya kware matuka a wannan aikin, yanzu haka yana kula da aikin jigilar ruwa a sansanin, ko wace rana, da sassafe, ya kan yi tafiyar sama da sa'o'i biyu don ya debo ruwa, kuma yanzu lokacin zafi ne, zafin ya kai kan ma'aunin digiri 50, amma, duk da haka bai hana shi wannan aiki ba.
A matsayina na shugaban rundunar sojojin kasar Sin dake yankin, Xiao Wei ya bayyana cewa, rundunar sojojin kasar Sin tana gudanar da aikin kiyaye zaman lafiyar MDD ne saboda kasar Sin tana sauke nauyinta dake wuyanta na babbar kasa a duniya, yana mai cewa, "Kasar Sin mamba ce ta MDD tun farkon kafuwarta, a don haka har kullum tana kare martaba da matsayin MDD, ta hanyar nuna kwazo da himma kan aikin kiyaye zaman lafiyarta, saboda wannan hakkin kasashe mambobin MDD ne, kana a matsayinta na zaunanniyar mambar kwamitin sulhun MDD, kasar Sin tana sauke nauyin dake wuyanta na babbar kasa a duniya, kamar yadda aka sani, zaman lafiya ya shafi ko wace kasa a fadin duniya, bil Adam suna da makoma guda daya, a don haka, ya dace kasashen duniya su hada kai domin gina kyakkyawar makomar bil Adam tare."
A karshe, Xiao Wei ya kara da cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin za su ci gaba da yin kokari matuka domin kammala aikin cikin nasara.(Jamila)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China