Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU: Annobar COVID-19 ta haifar da kalubaloli a tsarin ilmin Afrika
2020-09-21 10:43:46        cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU ta bayyana cewa bullar annobar COVID-19 ta kara ta'azzara tsarin ilmin nahiyar Afrika.

Da take bayyana matsalar da annobar COVID-19 ta haifarwa tsarin ilmin Afrika, hukumar gudanarwar ta AU ta jaddada cewa, akwai bukatar a bunkasa kirkire kirkire a dukkan fannonin ilmi, kana a rungumi tsarin juyin juya halin fasahohin cigaban zamani, domin kara tasirin bangaren da kuma tabbatar da ganin ba a bar wani rukunin marasa galihu a baya ba.

AU ta kuma kaddamar da wani shirin da zai duba hanyoyin samar da kirkire-kirkiren tsarin koyar da ilmi a duk fadin nahiyar Afrika, ta yadda za a samu damar rage illolin annobar ta COVID-19 a fannin ilmi.

Daga cikin sabon tsarin da ta kaddamar, hukumar ta AU ta bukaci a tallafawa shirin da kudi dalar Amurka 100,000.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China