Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yancin samun aikin yi daidai yake da 'yancin kare hakkin bil Adama
2020-09-18 19:54:39        cri

Samun aikin yi yana taimakawa wajen kiyaye mutuncin bil Adama, da ma ba da tabbaci ga hakkin bil Adama.

Jiya Alhamis, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da yadda ake kiyaye 'yancin samun aikin yi a jihar Xinjiang ta kasar Sin, wadda ta mai da hankali kan ainihin yanayin samun aikin yi a jihar, da aiwatar da manufofin samar da aikin yi, da nuna cikakken kwarin gwiwa ga ma'aikata game da samu aikin yi, da kuma tabbatar da hakkin 'yan kwadago, samu aikin yi yana tabbatar da rayuwa mai inganci, kamar yadda ake aiwatar da ayyukan kwadago na kasa da kasa da kuma hakkin bil Adam. Wadannan fannoni guda shida suna nuna kokarin jihar Xinjiang na mayar da inganta samar da aikin yi a matsayin babban aikin inganta rayuwa, mashahurin aikin tallafi, da ginshiki, kuma sun nuna hakikanin halin da jihar ke ciki na kiyaye ikon jama'ar kabilu daban daban wajen samun aikin yi.

Girmama da kaye hakkin bil Adama, shi ne babban tushen tsarin mulkin kasar Sin, ko da yaushe gwamnatin kasar na dora muhimmanci kan kiyaye ikon jama'arta na samun aikin yi, kana tana tsayawa wajen kawar da duk wani irin hanyar tilasta wa jama'a gudanar da aiki. Gwamnatin jihar Xinjiang tana ta sa himma wajen aiwatar da manufofin kwadago da na samar da aikin yi, da kokarin kare hakkin ma'aikata na samun aikin yi bisa doka.

A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, domin nuna wariyar akida da bukatunsu na adawa da kasar Sin, wasu rukunonin kasashen duniya sun yi biris da gagarumin kokarin da jihar Xinjiang ta yi na kare hakkin bil Adam, har ma suna daukar ma'auni biyu a wannan fannin na hakkin bil Adama. Haka kuma ba su yi la'akari da ainihin halin da ake ciki ba, kuma kuna shafa bakin fenti kan jihar Xinjiang, har ma sun ce wai "ana tilasta wa jama'ar jihar yin aiki", suna ta bata sunan jihar Xinjiang a fannin ba da tabbaci kan samun aikin yi, da nufin lalata 'yancin 'yan kabilu daban daban na jihar na samun aikin yi, ta yadda za su ci gaba da zama a wani hali na fama da talauci har abada, irin wannan matakin da wadannan masu adawa da kasar Sin suke dauka, martani ne ga neman kyakkyawar rayuwa mai kyau ga mutanen dukkan kabilun da ke Xinjiang, kuma ya kamata dukkan masu son adalci da neman ci gaba su nuna adawa sosai da matakin nasu

Aiki na kyautata zaman rayuwar jama'a, kuma aiki na samar da zaman alheri, a mataki na gaba, jihar Xinjiang za ta ci gaba da bin manufar dora muhimmanci kan jama'a, da ra'ayin mayar da aikin yi a matsayin babban tushen zaman rayuwa, kana da kara inganta samar da aikin yi, da tabbatar da ingancin aikin yi, za kuma ta kara kokari don biyan bukatun jama'ar kabilu daban daban na neman kyautatuwar zaman rayuwa, ta haka, za a aza harsashi mai kyau na tabbatar da zaman karko da tsaron al'umma cikin dogon lokaci. Ana cike da imanin cewa, jama'ar jihar Xinjiang za su kara jin dadin zaman rayuwarsu a nan gaba. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China