Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin, ita ce daya kacal a duniya da za ta samu karuwar tattalin arziki a bana
2020-09-17 13:59:01        cri

Jiya Laraba 16 ga wata, hukumar hadin gwiwa da raya tattalin arziki da ke da hedkwatarta a birnin Paris wato OECD, ta kaddamar da rahotonta game da hasashen tattalin arzikin duniya cikin matsakaicin lokaci, inda ta yi nuni da cewa, a bana tattalin arzikin duniya zai ragu da kashi 4.5 cikin kashi 100 baki daya. Kana hukumar ta yi hasashen cewa, daga cikin dukkan manyan rukunonin tattalin arzikin duniya, kasar Sin za ta samu karuwar tattalin arziki a bana, za ta kuma kasance daya kacal a cikin dukkan kasashe mambobin kungiyar G20.

Madam Margit Molnar, darektar ofishin kula da manufofin tattalin arzikin kasar Sin na hukumar OECD, wadda ta jagoranci ayyukan rubuta abubuwan da suka shafi tattalin arzikin kasar Sin, ta bayyana cewa, "Mun yi hasashen cewa, kasar Sin, ita ce kasa daya kacal a duniya, wadda za ta samu karuwar tattalin arziki a shekarar da muke ciki. Me ya sa hakan? Dalilai su ne, da farko alkaluman da muka samu ya zuwa yanzu dangane da harkokin tattalin arziki sun tabbatar da hakan. Na biyu kuma har zuwa yanzu, kasar Sin ita kadai ce a duniya da ta samu nasarar dakilewa, da kandagarkin yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19. Don haka tana samun farfadowa a sassa daban daban cikin hanzari. Alkaluman farkon rabin shekarar bana, da kuma na watan Yuli da Agusta, dukkansu sun tabbatar da farfadowar kasar Sin cikin farkon watanni 6 na bana. Saboda haka mun kyautata hasashenmu kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, har da kashi 4 da wani abu cikin kashi 100, gwargwadon hasashen da muka yi a watan Yuni."

Alkaluman da hukumar harkokin kididdiga ta kasar Sin ta gabatar a kwanan baya, dangane da tattalin arzikin kasar Sin na watan Agusta, sun shaida cewa, a karo na farko, kasar Sin ta samu karuwar tattalin arziki a wasu fannoni a bana.

To, shin ko kasar Sin za ta ci gaba da samun farfadowar tattalin arzikinta a karshen rabin shekarar da muke ciki? Madam Margit Molnar tana ganin cewa, zai yiwu ne kasar Sin ta cimma burinta. "A gani na, zai yiwu kasar Sin ta ci gaba da samun farfadowar tattalin arzikinta a karshen rabin shekarar bana, har ma ta wuce zaton mutane. Yanzu haka ta yi manyan sauye-sauye ga tsarin tattalin arzikinta. Alal misali, fasahar bayanai, da masana'antun manhaja sun kara kasonsu cikin tsarin tattalin arzikin kasar Sin, kuma haka lamarin yake a fannin hada-hadar kudi. Da ganin irin wannan babban sauyi, za a gane farfadowar tattalin arzikin kasar Sin ta yadda zai wuce zaton mutane."

Ko da madam Margit Molnar ta yaba wa yadda farfadowar tattalin arzikin kasar Sin ta wuce hasashen da aka yi, amma ta yi nuni da cewa, sakamakon barkewar annobar ta COVID-19, ya sa sana'o'in ba da hidima ba za su samu farfadowa cikin gajeren lokaci ba. Alal misali, dakunan cin abinci da otel-otel, wadanda suke samar da dimbin guraben ayyukan yi. Ta ce, kara samar da sabbin guraben aikin yi da tabbatar da karuwar kudin shiga, za su kara azama kan yin sayayya, ta yadda za a sa kaimi kan farfadowar tattalin arzikin kasar Sin ba tare da wata matsala ba.

A matsayinta na kasa ta biyu a duniya ta fuskar ci gaban tattalin arziki, mene ne tasirin da kasar Sin za ta yi kan farfadowar tattalin arzikin duniya? Madam Margit Molnar ta ce, yanzu wasu kasashe sun fara cin gajiyar farfadowar tattalin arzikin kasar Sin. "Yanzu haka mun fahimci cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin yana amfanar da wasu kasashen da suke samar da kayayyakin da ake sarrafawa. Alal misali, kasar Sin ta kara sayen karfen da ake sarrafawa, da tagulla da sauran nau'o'in kayayyakin da ake sarrafawa. Sa'an nan kuma, kasashen da suke kera hadadden allon taswirar layukan wuta, sun riga sun ci gajiyar saurin farfadowar tattalin arzikin kasar Sin, saboda kasar Sin tana kara sayen hadadden allon taswirar layukan wuta da yawa." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China