Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace a hana bangaranci ta hanyar amfanin manufar bangarori daban daban
2020-09-16 20:39:17        cri

A halin da ake ciki yanzu, annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a sauran sassan duniya, ana kuma sake amfanin da ra'ayin bangaranci da ba da kariya ga cinikayya a wasu kasashen duniya, to game da batun yadda bil Adam za su samu ci gaba, an samu amsa a babban taron MDD karo na 75 da aka kaddamar ta kafar bidiyo a jiya Talata, inda babban sakataren majalisar Antonio Guterres da shugaban babban taron majalisar karo na 75 Volkan Bozkir suka jaddada cewa, a yanayi mai sarkakiyar da ake ciki yanzu, ya dace kasashen duniya su nace kan manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, a maimakon nuna bangaranci, haka kuma ya dace a kara martaba matsayin MDD da rawar da take takawa.

A wannan rana kuma, kungiyar cinikayyar duniya ta yanke hukunci cewa, matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kara sanya haraji kan hajojin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 200 ya sabawa doka, hukunci mai adalci da kungiyar ta yanka ta samu amincewa matuka daga al'ummun kasashen duniya, har suna ganin cewa, hukuncin martani ne da manufar bangarori daban daban ta mayar wa ra'ayin na bangaranci.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, wasu 'yan siyasar Amurka suna siyasar duk wani al'amari, a sanadiyar haka, kasar ta Amurka take cin zaluncin sauran kasashen duniya kamar yadda take so, haka kuma tana lalata hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, alal misali, yayin da ake kokarin dakile annobar COVID-19 a fadin duniya, Amurka ta sanar da cewa, za ta fice daga hukumar lafiya ta duniya, har ma ta ki biyan kudin karo karo da yawansa ya kai dala miliyan 80 ga hukumar, kana ta dora laifin gaza hana yaduwar annobar ga wasu kasashe, ta kuma kwace kayayyakin kiwon lafiya daga hannun sauran kasashe, har ma ta yi yunkurin hana sauran kasashe su yi nazari kan allurar rigakafin annobar, duk wadannan sun nuna cewa, Amurka tana nuna kiyayya ga daukacin kasashen duniya.

Amma abun farin ciki shi ne, yawancin kasashen duniya suna yin adawa da matakan na Amurka, alkaluman binciken da MDD ta fitar sun nuna cewa, kaso 90 bisa dari na mutanen da aka zanta da su, suna ganin cewa, dole ne a gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa yayin da ake dakile annobar, kana kaso 74 bisa dari na mutanen sun dauka cewa, MDD tana taka babbar rawa a cikin harkokin duniya.

Don haka duniya tana matukar bukatar MDD mai karfi, dole ne kasashen duniya su hada kai domin hana nuna bangaranci, ta haka ne za a cimma burin samun kwanciyar hankali da wadata mai dorewa a fadin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China