2020-09-10 11:41:58 cri |
Yau ce ranar malamai ta kasar Sin karo na 36. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, "malaman da suka koyar mini suna da yawa, har yanzu na iya tunawa da kimarsu. Sun koyar mini ilmi, da ka'idojin zama nagartaccen mutum. Na ci gajiya sosai." Bayan ya zama shugaban kasar Sin, ya sha ziyartar jami'o'i da makarantun midil, inda ya gai da malamai da kuma yin hira tare da su. Mr. Xi ya bayyana cewa, idan ana son kammala wani babban shiri mai daukar tsawon lokaci, dole ne a dogaro kan ilmi. Idan ana son raya harkokin da suka shafi tarbiyya, dole ne a girmama malamai. Sabo da haka, an gane cewa, Xi Jinping ya dauki aikin ilmantarwa da muhimmanci da dole ne a raya shi yadda ya kamata. Ga rahoton game da yadda Xi Jinping yake ganin zumuncin dake tsakanin dalibai da malamai.
"Ina fatan malamai kuna cikin koshin lafiya. Ina farin ciki sosai da ganin malamanmu kuna lafiya sosai."
A jajibirin ranar malamai ta shekarar 2016, Xi Jinping ya koma Makarantar August 1st, inda ya yi karatun firamare da na sakandare na matakin farko a lokacin da yake karami, domin gai da dalibai da malamai. Lokacin da ga wasu tsoffin malaman da suka taba koyar da shi, shi da malaman dukkansu sun yi murna.
"Yau na dawo makarantarmu, kamar yadda na koma gida. Na je wasu wuraren da na taba zama domin tuna abubuwan da suka faru. Yanzu yanayin makarantar ya sauya sosai. Na kan tuna da lokacin da na yi karatu, da ilmin da malamai suka koyar mana. A duk inda na kai ziyara, na kan tuna da makarantarmu, bugu da kari, na kan yi mu'amala da makarantarmu."
Sannan a jajibirin ranar malamai ta shekarar 2014, Xi Jinping ya kai rangadin aiki a Jami'ar horar da malamai ta Beijing, inda ya sake jaddada muhimmacin aikin koyarwa. Ya bayyana cewa, malamai suna da muhimmanci, sabo da a lokacin da suke koyar da ilmi, suna kuma gyara halayyar da tarbiyar dalibai. Xi Jinping ya nuna cewa, tabbas nagartaccen malami yana da ilmi, da tausayi da da'a tare da kyakkyawan burin da yake son cimmawa.
"Ya kamata nagartaccen malami ya mayar da hankali kan aikin ilmantarwa, bai kamata a yi zaton cewa, aikin ba da ilmi wani aiki ne na neman kudin rayuwa kawai, aiki ne na gyara halayen dalibai. Duk wanda yake kokari a aikin koyarwa, tabbas zai samu kyakkyawan sakamako kamar yadda ake fata."
Bayan ya zama babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kuma shugaban kasar, sau da dama, Xi Jinping ya kan mika gaisuwa ga dukkan malaman kasar Sin. A ran 9 ga watan Satumban shekarar 2013, wato a jajibirin ranar malamai ta shekarar, a lokacin da shugaba Xi Jinping yake ziyarar aiki kasar Uzibikstan, ya aika wa dukkan malaman kasar Sin wata wasika, inda ya mika musu gaisuwa. Sannan a jajibirin ranar malamai ta shekarar 2014, ya kai rangadin aiki a jami'ar horar da malamai ta Beijing. A ran 9 ga watan Satumban shekarar 2015, ya ba da amsa ga wata wasikar da malamai wadanda suka fito daga lardin Guizhou, kuma suke samun karin ilmi a jami'ar horar da malamai ta Beijing suka aika masa. A ran 9 ga watan Satumban shekarar 2016, ya koma makarantar August 1, inda ya mika gaisuwa ga malamai da daliban makarantar. A jajibirin ranar malamai ta bana, shugaba Xi Jinping ya sake gabatar da wani jawabi, inda ya mika gaisuwa ga dukkan malamai da jami'an sashen aiki. Duk wadannan abubuwan da shugaba Xi Jinping ya yi sun bayyana yadda yake ba da muhimmanci ga malamai da harkar da ta shafi Ilimi.
A ran 10 ga watan Satumban shekarar 2018, gwamnatin kasar Sin ta shirya wani babban taron ilmantarwa na kasar, inda Xi Jinping ya jaddada cewa, a lokacin da ake kokarin bunkasa kasar Sin ta zamani mai bin tsarin gurguzu, ana fatan malamai za su kara kyautata halayensu, dukkan al'ummar Sinawa ma suna kara girmama malamai. (Sanusi Chen)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China