Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An buga tambarin dake alamta komawar kamfanonin sarrafa kayayyakin wasanni bakin aiki
2020-09-10 14:57:11        cri

A baya bayan nan, babbar hukumar kula da wasanni ta kasar Sin, ta fitar da tsarin aiki na bunkasawa, da kuma komawa bakin aiki, na kamfanonin dake samar da kayayyakin da ake amfani da su, a fannin wasanni bisa kimiyya da tsari managarci.

Wannan tsarin aiki na da nufin samar da manufofin komawa bakin aiki, da samar da kayan da ake bukata a fannin wasani, bisa yanayi da aka saba da shi, wanda zai ba da damar ci gaba da kandagarkin annobar COVID-19 da shawo kan cutar, ta yadda hakan zai haifar da yanayin farfadowa, da gudanar harkokin tattalin arziki, da zamantakewar al'umma yadda ya kamata.

Tsarin aikin na kunshe da ka'idoji, ciki hadda samar da tsarin kandagarki da shawo kan annoba bisa salon "Taro daya tsari daya", da kuma bude fannonin wasanni bayan samar da dukkanin matakai da ake bukata bisa tsari, wanda hakan zai shafi dukkanin wasanni, da farfado da dukkanin wasanni, da wuraren wasanni masu karbar mutane da yawa, manyan su da kananan su. Ga gasanni da dama, wannan alama ce mai kyau. Gasanni da kamfannin dake shirya su, da mayan ayyukan wasanni suna kara samun damar farfadowa yadda ya kamata.

A ranar 20 ga watan Yuni, hukumar wasan Kwando ajin maza ta kasar Sin ko CBA a takaice, ta kasance hukuma ta farko ta kwararrun 'yan wasa da ta buga gasa tsakanin kungiyoyi. Domin tabbatar da komai na tafiya daidai a fannin tsaron lafiya, hukumar CBA, da tallafin Zhong da 'yan tawagar sa, sun tsara cikakkun matakan kandagarki da na shawo kan annoba, da shirin gaggawa, da na tabbatar da ana aiwatar da matakai yadda ya kamata.

Yayin da aka tanaji matakai tabbatattu, na kandagarki da shawo kan cutar, an kuma tanaji matakan kimiyya na tabbatar da nasarar hakan. A ranar 25 ga watan Yuni, hukumar kwallon kafa ta Sin, za ta bude buga wasanni. Yayin da aka rage yawan wasanni, hukumar CSL ta raba kungiyoyin kasar 16 zuwa tukunoni 2. Inda za a buga zagayen wasanni 14 sau biyu-biyu, domin tantance zakaru cikin kulafliki masu buga gasar ajin kwaarru. Za a kuma tsara wasanni zango na biyu, su ma bisa tanajin dabarun kandagarki da na shawo kan cuta, da yanayin da aka samu game da gasar cin kofin duniya, da ta zakarun kungiyoyin Asiya ta AFC.

Kari kan hakan, kasancewar har yanzu akwai jami'an kungiyoyin kwallon kafar kasar da ba su koma kasar Sin din ba, hukumar ta tanaji dabarar daidaita tasirin irin wadannan jami'ai, yayin da ake buga wasanni.

Ana fatan dawo da buga manyan wasannin biyu, zai zama matakin bude sauran fannonin wasanni na kasar Sin baki daya. Bayan kammala shirye shirye cikin sama da shekaru 2, an tsara bude wasannin na kwallon tebur ko "Tennis" a birnin Anning na lardin Yunnan, tun daga 1 ga watan Agusta.

Domin tabbatar da gudanar wasanni ba tare da wata matsala ba, an yi gwajin wasu wasannin a cikin watan Yuli. Dukkanin 'yan wasan kananan masu kwarewa ne daga birnin Kunming, amma ba a rage matakin gudanar da wasannin da aka buga ba. An gwada nagartar dukkanin tsarin gasar, hade da kandagarki da aikin shawo kan cuta, da tsarin watsa shi ta kafar talabijin, da bunkasa fannin kasuwanci, da hidimomin masu motsa jiki da masu horas da 'yan wasa, wanda hakan ya samar da ginshikin bude manyan gasanni a hukumance.

Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin babban daraktan kula da wasan Tennis na kasar Sin, karkashin babbar hukumar wasanni na kasar Huang Wei, ya ce batun kare lafiya na daukacin masu shiga wasanni shi ne kan gaba, kuma gwajin wasan da aka yi ya haifar da kyakkyawan sakamako a fannin kiyaye dabarun kandagarki da shawo kan cutar.

Jami'in ya kara da cewa "Muna da karfin gwiwar cewa, an yi la'akari da dukkanin dabarun shawo kan annoba, da kandagarkin ta yayin da ake gudanar da wasanni, kuma hukumar shirya gasar kwallon tebur za ta shirya wasanni masu kayatarwa ga 'yan kallo.

A yanzu haka, tsarin kasa da kasa na kandagarki da shawo kan cutar COVID-19 na fuskantar kalubale. Don haka tsarin aikin da aka tanada, na kira da a aiwatar da matakan kimiyya, don tunkarar tasirin dage ka'idojin kebe mutane a kasashen yammacin duniya, da ma yankunan da za a gudanar da gasar Olympic ta lokacin sanyi ta birnin Beijing. Alal hakika, ba bu wata gasar kasa da kasa mai muhimmanci, wadda za ta gudana cikin wannan shekara ta bana, in banda gwajin gasar Olympic ta Beijing ta lokacin sanyi da aka yi.

Sake bude kamfanonin sarrafa kayayyakin wasanni

A cewar daraktar cibiyar bincike da raya fannin masana'antun sarrafa kayayyakin wasanni a jami'ar Tsinghua ta kasar Sin Wang Xueli, haduwar 'yan kallo da cudanyar su, muhimmin bangare ne a fannin gasanni, hakan yana kuma zaburar da su kan su 'yan wasa. Don haka, ana fatan sake dawo da damar shigar 'yan kallo filayen wasa sannu a hankali, ta yadda 'yan kallo za su kalli wasanni a filaye, tare da kiyaye ka'idojin kandagarki da na shawo kan annoba yadda ya kamata. Jami'ar ta ce, ana iya kiyaye yawan 'yan kallo da za su shiga filayen wasa, kamar barin adadin da bai wuce kaso 50 bisa dari na 'yan kallo su shiga filin wasa ba, sa'an nan za a rika daidaita adadin gwargwadon yanayin da ake ciki, bisa hadari ko matakan kandagarki da shawo kan annobar da ake fuskanta, a wuraren da ake gudanar da wasannin.

Wang ya ce, wani abun tambaya da masu sha'awar wasanni ke ambata shi ne, ta yaya za a kara samar da nishadi a sha'anin wasanni ba tare da 'yan kallo na samun shiga filayen wasanni ba? Domin amsa wannan bukata, hukumar kwallon kafa ta kasar Sin, da hadin gwiwar masu mallakar ikon nuna wasanni, na fatan amfani da wasu fasahohi don kirkirar hotunan fasaha da za su cike wuraren 'yan kallo da babu kowa, a yayin da aka bude sabuwar kakar wasanni. Kaza lika fasahar za ta rika bayar da sautin shewar 'yan wasa da suka taba shiga filayen wasanni a baya, inda za a saka su cikin wasanni da za a yi nan gaba yayin da ake nunawa 'yan kallo ta kafar talabijin, su kuma da ce da yanayin sabbin wasanni. Duka dai wannan matakai na nufin samar da yanayi mai nishadantarwa ga masu kallon wasanni, da kayarta da bidiyon wasannin da za a rika watsawa ta talabijin, da kuma kara nishadantar da 'yan kallo.

Jami'ar ta kara da cewa, fannin kayatar da 'yan kallo muhimmi ne ga kamfanonin dake tsara wasanni. Fara bude fannonin wasanni, ya kara ingiza bude masana'antun sarrafa kayayyakin wasanni, da sauran fannoni masu nasaba da su, kamar masu tallata hajojin su, da masu watsa labarai a fannin, da ma fannin shakatawa, wadannan dukkanin su ke da kasuwa mai matukar girma.

A nasa bangaren, mamba a zaunannen kwamitin wasanni na gundumar Duolun ta jihar Mongolia ta gida He Mingjian, ya ce tun daga ran 25 ga watan Yuli, aka bude gasar tseren kekuna ta 14 ta Circum zuwa Duolun, a gundumar ta Duolun, gasar da aka yiwa lakabi da "Xilin Gol League". Mr. He Mingjian, wanda kuma shi ne mataimakin babban jagoran gundumar ta Duolun, ya ce baya ga muhimmancin gudanar da wannan gasa, bayan an sha fama da COVID-19, wanda hakan ya matso da gasar kusa da jama'a, a hannu guda, hakan ya bunkasa harkokin yawon bude ido a yankin, ta hanyar hade sassan wasannin da yawon shakatawa.

An yi imanin cewa, bullar wannan annoba yayi matukar tasiri tsakanin wasu kamfanonin sarrafa kayayyakin wasanni, kuma ko shakka babu, kamfanonin dake ayyuka a fannin bunkasa tallace tallace, da na gine gine, za su fuskanci wahalhalu, ko damuwa game da matakan da ake aiwatarwa, na komawa aiki da sarrafa hajoji. Don haka akwai bukatar kananan hukumomi a dukkanin matakai, su shiga aikin tabbatar da nasarar tsarin aiki da aka fito da shi, don karfafa manufofi na ingiza nasarar irin wadannan kamfanoni, ta yadda za su samu sassauci wajen farfadowar su.

Sannu a hankali an fara bude wasanni masu kunshe da mutane da dama

Daraktan hukumar raya wasanni a lardin Xiamen, ya zagaya da masu sha'awar wasanni zuwa sassan wuraren da za a gudanar da wasanni cikin su ta kafar bidiyo kai tsaye, inda ya fayyace yadda aka tsara gudanar da wasanni nan gaba. A nata bangare, kungiyar wasan zamiya a ruwa, ta kaddamar da kwasa-kwasai 52, don yayata wannan wasa, da ba da damar zurfafa fahimtarsa yadda ya kamata, kwasa kwasan da suka samu masu kallo kusan 100,000. Yayin da ake tsaka da aiwatar da matakan kandagarki da na shawo kan cutar, wasanni sun kasance muhimman bangarorin jin dadin jama'a, an kuma gudanar da gasanni daban daban ta kafar yanar gizo.

Ta hanyar ci gaba da kyautata matakan kandagarki da na shawo kan cutar COVID-19 a dukkanin sassan kasar Sin, ana ci gaba da gudanar da wasanni a filaye na zahiri sannu a hankali bisa tsari. Kaza lika kaddamar da tsarin aiki, ya sanya an samu karin dama ta shirya bude karin wasanni da cikakken karfin gwiwa. Yanzu haka ma, an tsara bude gasar wasan zamiya a ruwa ta shekarar 2020 ajin matasa a birnin Shenzhen, tun daga ranar 27 ga watan Yuli. Tuni kuma matasa da yawa masu sha'awar shiga wannan gasa, suka nuna sha'awar su ta shiga a fafata da su.

A wani bangaren kuma, za a kaddamar da gasar wasan kwallon Kwando ta mutane uku-uku, domin nishadantar da 'yan kallo. Shugaban hukumar dake lura da wannan nau'i na wasa, a hukumar kwallon Kwando ta Sin Chai Wensheng, ya ce za a samar da dukkanin abubuwan da ake bukata domin bunkasa wannan wasa, cikin watanni 6 na karshen shekarar nan, matakin da ake sa ran zai taimaka wajen shigar da karin mutane masu kwazo cikin wannan wasa.

An tsara shigar mambobi uku daga babbar kungiyar kwallon Kwando ta Sin cikin wannan gasa, ta yadda hakan zai samar da armashi sosai ga gasar. A hannu guda kuma, karin 'yan wasa za su samu kwarewa; A karfafa karsashin kananan hukumomi a fannin shirya gasanni makamanta, da samar da bayanai game da nasarar shirin.

Yayin da ake tsaka da dawowa wasanni, da bude dukkanin sassa masu alaka da hakan, ya dace a maida hankali ga bin ka'idar farfadowa sannu a hankali. A wannan lokaci na zafi, adadin wuraren linkaya dake bude a birni Shanghai sun ragu da kaso 15 bisa dari, idan an kwatanta da wadanda ke bude a irin wannan lokaci a bara. Domin tabbatar da ana bin ka'idojin kandagarki da shawo kan annobar COVID-19, an fadada wuraren linkaya na ko wane mutum daya, daga sakwaya mita 2.5 zuwa sakwaya mita 5, yayin da kuma ake lura da adadin mutanen dake shiga irin wadannan wurare na linkaya.

Mr. Wang ya ce, Sin ta samu kwarewa sosai a fannin yaki da annoba, ta yadda aka samu damar dawowa harkokin wasannin motsa jiki, da wasanni masu hada jama'a da dama cikin kwanciyar hankali. Sake bude filayen wasanni, baya ga karfafa fannin da ya yi, a hannu guda kuma, alama ce dake nuna cewa, sannu a hankali, yanayin zamantakewar al'umma na dawowa yadda aka saba kafin bullar wannan cuta.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China