2020-09-09 10:21:02 cri |
Shugaban babban taron MDD mai barin gado, Tijjani Muhammed-Bande, ya bukaci kasashe mambobin majalisar, da su mutunta dokokin kasa da kasa.
Da yake amsa tambayar manema labarai, a karshen wa'adin aikinsa, kan yadda wasu kasashe ke nuna girman kan game da kasancewar bangarori daban-daban, da keta dokokin kasa da kasa, Muhammed-Bande ya ce, MDD ta fayyace komai game da wajibicin mutunta dokoki na kasa da kasa.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China