Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ruhin yaki da cutar COVID-19 karfin Sinawa ne na tinkarar mawuyancin hali
2020-09-08 21:29:24        cri

Da safiyar yau Talata ne aka gudanar da gaggarumin bikin karrama wadanda suka taimaka wajen dakile cutar COVID-19 a kasar Sin, a babban dakin taruwar jama'ar kasar Sin dake birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya mika musu lambobin yabo, tare da ba da jawabi.

A cikin jawabinsa ya ce, za a sadaukar da komai don ba da tabbaci ga rayukan jama'a, kuma abubuwan da ya fadi na bayyana tunanin JKS ta fuskar gudanar da harkokin kasar, wato maida jama'a a gaban komai.

Ya ce hadin kai hanya ce mafi kyau wajen yakar cutar, kuma Sinawa da yawansu ya zarce biliyan 1.4, suna kokarin hada kansu don tinkarar mawuyancin hali, matakin da ya jawo hankalin kasa da kasa.

Masu aikin jiyya fiye da dubu 40, sun tafi birnin Wuhan don ba da taimako, masu aiki a unguwo'i fiye da miliyan 4, sun yi aiki ba dare ba rana, kana masu kimiyya sun yi kokari gudanar da aiki na nazari. Ban da wannan kuma, sauran masu sana'o'i sun yi iyakacin kokarin gudanar da ayyukansu, matakan da suka zama dalilin da ya sa Sin ta iya samun nasarar dakile wannan mummunar cuta a cikin watanni 3 kacal. Kaza lika ta zama kasa ta farko da ta kai ga farfadowa daga illar da cutar ta haifar mata.

Bugu da kari, kasar Sin tana sahun gaba a duniya, ta fuskar kandagarkin cutar, da farfado da tattalin arziki, wanda hakan ya bayyana karfinta na samun farfadowa mai inganci, da ma kuzarin samun bunkasuwa mai armashi.

A halin yanzu dai, cutar na ci gaba da dabaibaye duk fadin duniya. Jama'ar kasar Sin na kokarin ba da taimako ga al'ummar duniya. Alal misali; Sin ta sanar, da baiwa WHO tallafin kudi har dala miliyan 50, da ma tura rukunonin masana 34 zuwa kasashe 32, da ma samar da kayayyakin tallafi sau 283 ga kasashe 150, da kungiyoyin kasa da kasa 4. Ban da wannan kuma, ta samar, ko fitar da kayayyakin kandagarki ga kasashe ko yankuna fiye da 200 da dai sauransu, matakan da suka taimaka wajen ceton duban rayukan jama'ar duniya.

Darektan cibiyar nazarin kasar Sin ta Argentina Ignacio Villagran ya ce, Sin ta zama abin misali wajen yakar cutar, ta kuma baiwa sauran kasashe taimakon ta na samun nasarar magance cutar, matakin da ya bayyana ainihin tunanin raya kyakkyawwar makomar Bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China