Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Aikin yaki da cutar COVID-19 ya shaida fifikon tsarin kasar Sin
2020-09-08 16:28:42        cri
A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a gun taron mika lambobin yabo ga wadanda suka taka rawa a yaki da COVID-19 cewa, aikin yaki da cutar a wannan karo ya shaida fifikon tsarin kasar Sin da tsarin tafiyar da harkokin kasa. Yayin da ake kokarin tabbatar da tsaron rayukan jama'a, tilas ne jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi namijin kokari da sadaukar da rai kan aikin, domin manufar jam'iyyar ita ce samar da hidima ga jama'a a dukkan fannoni.

Xi Jinping ya bayyana cewa, a yayin da aka shiga mawuyacin hali na yaki da cutar, an dakatar da wasu ayyukan raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, amma hakan bai kawo babbar illa ga zaman rayuwar jama'a ba, kuma an kiyaye tsarin zamantakewar al'ummar kasar yadda ya kamata. Dalilin da ya sa aka samu wannan shi ne Sin tana da karfi tun kafuwar sabuwar kasar Sin, musamman bayan da aka yi kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje.

Kasar Sin za ta ci gaba da bin tunanin al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da yin kokari tare da kasa da kasa wajen tinkarar kalubalen duniya. Sin za ta fadada hadin gwiwar samun moriyar juna tsakaninta da kasashen duniya, da ci gaba da sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, da tabbatar da tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, da kiyaye tsarin samar da kayayyakin duniya yadda ya kamata, don kokarin farfado da tattalin arzikin duniya cikin hanzari. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China