Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Saudiyya ta sanar da gano sabbin rijiyoyin mai da iskar gas
2020-08-31 10:23:25        cri
Ministan makamashi na Saudiyya, Abdulaziz bin Salman Al Saud, ya sanar a jiya cewa, an gano sabbin rijiyoyin mai da gas biyu a kasar.

Kamfanin mai na kasar, wato Saudi Aramco ne ya gano rijiyoyin biyu da suka hada da rijiyar hadat Al-Hajrah a yankin Al Jawf da kuma rijiyar Abraq Al-Talul dake yankin iyakar kasar na arewaci.

Kamfanin Saudi Aramco zai tantance adadin mai da gas a rijiyoyin biyu, tare da hako karin rijiyoyi domin tantance fadinsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China