Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kalamar "yanke hulda" tamkar wata guba ce da wasu 'yan siyasar Amurka suke shayar da kamfanonin kasarsu
2020-08-29 21:03:01        cri
A tattaunawar da aka gudanar a kwanan nan, shugabannin kasar Amurka sun sha furta kalmar "yanke hulda" da kasar Sin, suna cewa wai Amurka ba lallai ne ta yi huldar cinikayya da kasar Sin ba.

A watannin baya bayan nan, 'yan siyasar Amurka sun sha yin makamanciyar wannan muhawara daga lokaci zuwa lokaci, amma dai wata barazana ce kawai da ta da kurar siyasa ganin cewar shekarar zaben kasar ta kama.

Za a iya hana kamfanonin Amurka yin kasuwanci da kasar Sin? Wannan cece-kucen 'yan siyasar Amurkan kamar wata guba ce da suke shayarwa, wanda kamfanonin Amurka sun riga sun saba jinta. Batu na baya bayan nan shi ne wanda ke cewa, a kwanan nan gwamnatin Amurka ta fitar da dokar ofishin shugaban kasa wanda take cewa daga ranar 20 ga watan Satumba, daidaikun Amurkawa da kamfanonin kasar an haramta musu ta'ammali da manhajar WeChat wajen ake yin hada-hadar kasuwanci da kuma babban kamfanin nan na kasar Sin Tencent. A sakamakon hakan, ake sa ran yiwuwar mayar da martani daga kamfanonin Amurka irin su Apple, Ford, Goldman Sachs, Wal-Mart, P&G.

WeChat yana da masu hulda da shi sama da mutane biliyan daya a fadin duniya, kuma shi ne babbar manhajar da ake amfani da ita wajen al'amurran sadarwa a kasar Sin. Ayyukanta ya shafi kasuwanci, sadarwa, ciniki na zamani, biyan kudade da makamatansu, yana taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwancin kasar Sin. Mujallar kasuwanci ta Burtaniya "Financial Times" ta yi tsokaci a karon farko inda ta ce matakin gwamnatin Amurkar na yin haramtar babbar illa ce ga kamfanonin fasahar zamani na kasar Sin, amma a hannu guda kuma, zai yi illa mafi muni ga kamfanonin Amurka har ma za su fi shan wahala kan matakin.

Wani abin ban sha'awa shi ne, duk da kasancewar 'yan siyasar Amurka sun sha nanata batun "yanke hulda", amma suna shan matsin lamba daga bangaren 'yan kasuwa, ya kamata su kyautata halayyarsu. A kwanan nan kamfanin Bloomberg ya bada labari da dumi duminsa. Ya ce mutane da yawa sun fahimci yadda lamarin yake, kasancewar makonni biyu bayan da gwamnatin Amurka ta ba da sanarwar yin haramcin, wasu jami'an Amurka cikin sirri sun tuntubi kamfanonin Amurka da dama, da suka hada da kamfanin Apple, sun jaddada cewa za su iya ci gaba da yin hulda da kasar Sin ta hanyar manhajar WeChat. Wannan na kara tabbatar da cewa kalmar "yanke hulda" ba wata magana ba ce face wasan kwaikwayo wanda 'yan siyasar Amurke ke yi wadanda ke neman darewa madafun iko. Wannan wata yaudara ce kawai wanda za a iya gane hakan a nan gaba.

A tsarin tattalin arzikin da duniya ke amfani da shi a wannan lokaci, babu wata kasa da za ta iya dogaro da kanta ita kadai. Musamman a bayan annobar COVID-19, dukkan kasashen duniya suna da tsananin bukatar dawowa bakin aiki da samar da kayayyaki, da farfadowar harkokin tattalin arziki, da kuma tabbatar da dorewar ayyukan masana'antu wajen samar da kayayyaki da cinikayyarsu. A wannan mataki, kasashen duniya za su iya kai gaci ne kadai idan sun yi cudanya da takwarorinsu. Mujallsar Burtaniya "Economist" ta bayyana cewa, takaddamar ciniki tsakanin kamfanonin Sin da na Amurka zai kawo illa ga kowa. Ko ma dai mene ne, akwai yiwuwar kamfanonin Amurka ne za su fi shan wahala mai tsanani. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China