Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurkawa sun yi zanga-zanga domin nuna adawa ga wariyar launin fata
2020-08-29 16:15:56        cri

A jiya Juma'a Amurkawa sama da dubu gomai sun yi zanga zanga mai taken "matsar da gwiwarka daga wuyanmu" a kusa da dakin tunawa da Lincoln dake birnin Washington domin nuna adawa ga wariyar launin fata da matakin nuna karfin tuwo da 'yan sandan kasar suka dauka kan tsirarun al'ummun kasar.

Yayin taron a jiya, dangogin shugaban jagorancin aikin neman samun hakkin bakar fata Martin Luther King, da matashin nan bakar fata George Floyd da ya rasu sakamakon makare shi da gwiwa da wani 'dan sanda farar fata ya yi a watan Mayun bana, da matashi bakar fata Jacob Blake da ya kasance nakasa sakamakon harbin bindigar da wani 'dan sanda farar fata ya yi masa, da sauransu.

Dan gidan Martin Luther King ya furta cewa, makasudin shirya zanga zangar shi ne domin kawar da laifuffuka guda uku wato talauci da kabilanci da kuma nuna karfin tuwo da mahaifinsa ya gabatar kafin shekaru 57 da suka gabata, a cewarsa, ci gaban da aka samu bayan kokarin da aka yi a shekarun 1960, ya sake shiga yanayin hadari, dole ne bakar fata su yi kokarin kiyaye zaman walwala da marigayin suka kafa tushensa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China