Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dabarun Sin za su taimakawa ci gaban kasashen dake bakin kogin Lancang da na Meigong
2020-08-25 20:12:38        cri

A jiya Litinin ne aka kira taron shugabannin kasashe shida, wato Sin da Myamar da Laos, da Thailand da Kambodia, da Vietnam, game da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen bakin kogin Lancang da na Meigong karo na uku ta kafar bidiyo, inda firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da shawarwari a bangarori guda shida, wadanda suka hada da yadda za a kara karfafa hadin gwiwa wajen amfani da albarkatun ruwa, da yadda za a kara habaka hadin gwiwar cinikayya, da yadda za a kara karfafa cudanyar juna.

Sauran fannonin sun kunshi yadda za a kara zurfafa hadin gwiwa domin samun dauwamammen ci gaba, da yadda za a gudanar da hadin gwiwa a bangaren kyautata rayuwar al'ummun kasashen, da kuma yadda za a aiwatar da manufar kara bude kofa ga ketare tare da yin hakurin juna, domin taimakawa kasashen dake bakin kogin Lancang da na Meigong wajen dakile rikici da kalubalen da suke fuskantar, tare kuma da samun ci gaba tare.

Bayan taron shugabannin, an fitar da sanarwar Vientiane, hedkwatar kasar Laos, inda aka sanar da cewa, kasashen shida za su kara karfafa huldar sada zumunta ta hadin gwiwar siyasa da tsaro, da tattalin arziki, da cudanyar al'adu, da kuma huldar sada zumunta ta tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen dake bakin kogin Lancang da na Meigong. Kuma ko shakka babu taron zai ingiza hadin gwiwarsu a nan gaba.

Tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen nan shida, tsari ne mai sabon salo na shiyya shiyya, wanda ake gudanarwa bisa tushen moriyar juna, bayan kokarin da suke a cikin shekaru hudu da suka gabata, tsarin da aka cimma ya riga ya samu babban sakamako ta fuskokin aikin gona, da yaki da talauci, da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da amfanin albarkatun ruwa da sauransu. Haka kuma al'ummun kasashen suna amfanin sakamakon matuka.

Idan an kwatanta taron jiya da tarukan da aka kira a baya, za a lura cewa, an kira taron ne karkashin yanayi na musamman, saboda yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 tana haifar da tasiri ga daukacin duniya, don haka ya dace kasashen dake bakin kogin Lancang da na Meigong su yi kokarin neman samun mafita.

A kwanakin baya bayan nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba gabatar da shawarar cewa, kamata ya yi kasashe daban daban su yi kokari domin kara karfafa hadin gwiwar shiyya shiyya. Yanzu haka kasar Sin ta fitar da dabarunta, tabbas ne dabarun za su taimakawa kasashen yayin da suke gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu, haka kuma za su samar da karin damammaki ga al'ummun kasashen baki daya.

Hakika gudanar da hadin gwiwa zai amfanin bangarori daban daban, kasar Sin da sauran kasashen dake bakin kogin aminai ne, wadanda za su ci gaba da sanya kokari tare, domin ingiza hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China