2020-08-25 11:18:50 cri |
Tun barkewar cutar, Sin ta nace wajen gaggauta aikin binciken samar da allurar ta hanyoyi daban-daban. Yanzu kuma, kamfanoni biyu dake nazari da kuma samar da allurar sun bayyana a nan birnin Beijing kwanan baya cewa, yanzu haka an shiga mataki na uku na aikin gwajin amfanin wannan allura, watakila zai kai zuwa karshen wannan shekara.
Rahotanni na cewa, kamfanin CNBG na kasar Sin ya gwada allurar riga kafin da ya samar a mataki na uku a kasashe hadaddiyar daular Larabawa UAE da Peru da Morocco da dai sauransu. Kamfanin Sinovac Biotech Ltd ya samu iznin aikin gwaji a mataki na 3 a Indonesiya a watan Yuli da ya gabata, Ya kuma fara gudanar da wannan aiki a birnin Bandung na lardin yammacin Jaba tun daga watan Agusta. Ban da wannna kuma, kamfanin ya gudanar da mataki na 3 na gwajin riga kafin a cibiyoyi 12 a jihohi 6 na Brazil, inda aka tattara masu sa kai 9000, da suka amince za su shiga wannan aiki daga watan Satumba mai zuwa.
Mataimakin shugaban CNBG Zhang Yuntao ya ce, aikin nazarin allurar riga kafin COVID-19 da ake gudanarwa bisa kimiya da fasaha a fannoni daban-daban, yana tafiya cikin sauri, idan aka kwatanta da aikin nazarin sauran alluran rigakafi. Da zarar an fara amfani da ma'aikatan harhada allurar a sassan Beijing da Wuhan na kamfanin, za a iya samar da allurar rigakafi miliyan 220 a ko wace shekara. Shugaban hukumar zartaswa kana shugaban kamfanin Sinovac Biotech Ltd. Yin Weidong ya nuna cewa, kafin watan Agusta da muke ciki, reshen kamfanin mai fadin muraba'in mita dubu 70, zai fara samar da allurar riga kafi, inda yake zai samar da allurar miliyan 300 a ko wace shekara.
Ba kasar Sin ce kawai take kokarin nazari da samar da riga kafin ba, akwai wasu kamfanonin kasashen duniya da suma suke gaggauta wannan aiki. Hukumar WHO ta taba yin hasashe cewa, aikin nazari da samar da allurar riga kafin zai kwashe watanni 12 zuwa 19 inda babu wata babbar matsala. Amma, hukumar ta bayyana cewa, yanzu haka duniya ta himmatu kan wannan aiki, har zuwa ran 20 ga watan nan, allurar da ake yin nazari kuma an gabatarwa WHO ya kai 30, daga cikinsu guda 6 sun shiga mataki na 3 na gwajin, kasar Sin tana guda 3 daga cikinsu, daya daga Amurka, daya daga Biraniya, sai Jamus da Amurka dake guda daya kowanne. Kazalika, akwai wasu alluran riga kafin 139 da ake tantance su.. Ban da Sin da Amurka wadanda suke sahun gaba a wannan fanni, kasashen Rasha da Indiya da sauransu suna gaggauta wannan aiki. Kafofin yaba labarai na kasar Rasha sun bayyana cewa, hukumomi 17 na kasar suna kokarin nazarin nau'o'i 26 na alluran rigan da kasar ta samar, daga cikinsu Sputnik V ya fi sauri. Firaministan kasar Indiya, Narendra Damodardas Modi ya bayyana a kwanan baya cewa, kasarsa tana binciken nau'o'i 3 na riga kafain da ta samar mataki-mataki. Ministan kiwon lafiyar kasar Harsh Vardhan ya ce, za a samar da allurar kafin karshen shekara.
WHO ta yi kira ga kasashe daban-daban da su kara hada kai don yin nazari da samar da riga kafi don kaucewa yin takara, ta wannan hanya kasashe daban-daban za su kaucewa duk wani hadari da cin moriya tare da kuma fito da allura mafi inganci.
Aikin gwajin allurar na da muhimmanci matuka, mataki na 3 shi ne gwaji na karshe da za a yi kafin a samar da wannan allura, a don haka, akwai bukatar samun masu aikin sa kai da dama, don gano ingancin wannan allura. Yanzu, ana gudanar da wannan aiki a kasashen Brazil da Amurka da Afrika ta kudu da dai sauransu, wuraren da suke fi fama da wannan cutar, abin da ake bukata shi ne "Hadin kan kasa da kasa".
Babban sakataren WHO Tedros Adhanon Ghebreyesus ya shedawa manema labarai a kwanan baya cewa, yana sa ran duniya za ta kawo karshen cutar cikin shekaru biyu masu zuwa, kuma hanya daya tilo da za a bi ita ce, hadin kan kasa da kasa, babu wata kasa ita kadai da za ta tinkari wannan cuta. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China