2020-08-24 09:56:15 cri |
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada bukatar gudanar da aiki mai inganci yayin da ake dakile ambaliya da rage radadin bala'i gami da sake ginawa da dawo da harkoki. A hannau guda kuma, a ci gaba da kara kokari wajen farfado da tattalin arziki, yayin da ake aiwatar da gyare-gyare da kara bude kofa.
Li ya bayyana haka ne yayin da yake rangadi a birnin Chongqing dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin da matsalar ambaliyar ruwa ta shafa, inda ya ziyarci gidajen mazauna kauyuka, don ganewa idonsa irin barnar da ambaliyar ta yi musu, da matsugunin wucin gadi don ganin yadda mutanen da aka tsugunar a wurin suke rayuwa. Ya bukaci hukumomin wurin da su kara agazawa kamfanonin samar da kayayyaki dake wurin, ta yadda za su farfado cikin sauri.
A lokacin da ya ziyarci kamfanonin dake yankin, Li ya bayyana cewa, kwazon kananan kamfanonin kasar a 'yan watannin nan ya nuna irin kyakkyawan tasirin da hakan ya haifar. Yana mai cewa, idan har aka tabbatar da tsaron cin gashin sama da kasuwanni miliyan 100, da cika alkawarin kara samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 9 a birane a wannan shekara, hakika, kasar Sin za ta samu bunkasar tattalin arziki da take fatan samu a shekara.
Li ya kara da cewa, ya kamata a kara zaga damtse ta yadda za a iya magance duk wani rashin tabbas da ka iya kunno kai, yayin da ake kokarin neman bunkasuwa. (Ibrahim Yaya)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China