Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira ga Amurka da ta dakatar da gallazawa kamfanonin kasarta
2020-08-21 10:41:22        cri

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta yi kira ga Amurka da ta dakatar da gallazawa kamfanonin Sin, maimakon haka a cewar ma'aikatar, kamata ya yi Amurkan ta maida hankali, wajen aiwatar da matakan inganta hadin gwiwar sassan biyu, ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da ma kyautata zamantakewar al'ummun su.

Da yake gabatar da wannan kira a jiya Alhamis, yayin ganawa da manema labarai a birnin Beijing, kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce Amurka ta shafe tsawon lokaci tana fakewa da batun tsaron kasa, da bukatar gaggawa ta kasa, wajen sanya tarnaki, ko hana kamfanonin kasar Sin gudanar da harkokin su na zuba jari da cinikayya a Amurka. Ta kuma sha kakabawa kamfanonin Sin takunkumi ba tare da wasu sahihan dalilai da za su iya samun goyon bayan doka ba.

Mr. Gao na wannan tsokaci ne, yayin da aka tabo batun haramcin ci gaba da harkoki, da mahukuntan Amurka suka kakabawa manhajar musayar bidiyo ta TikTok, wadda kamfanin Sin ke gudanarwa. Ya kuma ce irin wadannan matakai na Amurka, suna gurgunta halastaccen ikon kasuwanci na irin wadannan kamfanoni.

Daga nan sai ya bayyana matakan kakaba takunkumi, da gallazawar da wadannan kamfanoni ke fuskanta, a matsayin dalilan da ka iya sanyaya gwiwar masu fatan zuba jari a Amurka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China