Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin 'yan bindiga ya yi sanadin mutuwar mutane 11 a Nijeriya
2020-08-20 10:10:51        cri

Hare-haren 'yan bindiga da aka shafe wasu kwanaki ana kai wa kauyukan jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya, sun yi sanadin kisan akalla mutane 11.

Cikin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai tsakanin ranar 16 zuwa 18 ga wata, a yankunan Zangon Kataf da Kajuru da Kachia dake kudancin jihar, har da shugaban wani kauye.

A cewar wata sanarwa da kungiyar kawance ta al'ummar kudancin Kaduna (SOKAPU), wadda ke kunshe da kabilu 67 na kudancin jihar, hare-haren sun kuma jikkata mutane tare da kone gidaje da dama.

Sanarwar ta ce an kashe galibin mutanen ne yayin da suke gona ko kuma aka yi musu kwantar bauna, tana mai cewa, maharan sun fito ne daga dazukan dake kusa da yankunan, sannan kuma sun yi wa mazauna sata.

Zuwa yanzu dai, rundunar 'yan sandan jihar ba ta fitar da sanarwa dangane da hare-haren ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China