Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sha'anin al' adu ya zama sabuwar hanyar raya kauyukan kasar Sin
2020-08-18 15:48:55        cri

A da, kauyen Longtan na gundumar Pingnan na birnin Ningde dake lardin Fujian na kasar Sin, kauye ne mai matukar talauci, inda dukkan matasan kauyen suka fita waje don neman aikin yi. A shekarun baya-baya nan, an yi wa tsoffin gine-gine gyaran fuska don raya sha'anin al'adu, kana an gina dakunan zane-zane da shan shayi da dama, matakin da ya dawo da matasa cikin kauyen.

"Wannan kauyen ya yi kyau sosai, mazauna kan iya magana da Turanci. Har wata tsofuwa mai shekaru 87 a duniya ta iya jimloli 6 da Turanci kamar su Hello. Na kashe yawancin lokacina a wannan wuri, ba na son komawa garinmu a birnin Hangzhou, saboda zaman rayuwa a nan yana da dadi matuka."

Wannan wata mace ce mai suna Meihong da ta mallaki wani dakin zane-zane. A shekarar 2018 ta yi murabus daga matsayin malamar makaranta ta zo nan kauyen Longtan don bude wannan dakin zane-zane. A cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata, ta tafiyar da harkokinta yadda ya kamata. An gudanar da sha'anoni daban-daban dake da alaka da al'adu a wannan wuri har ya zama wani salon zaman rayuwar wurin.

Amma, a shekaru 3 da suka gabata, halin da ake ciki ya bambanta. Saboda karancin gonaki da cunkuson mutane, an samu koma bayan tattalin arziki a wurin, matasan wuri sun fita waje don neman aikin yi, wasu kuma sun kaura zuwa wasu wurare. Chen Xiaolan, mazauniyar wannan kauye ta ce:

"Wani lokaci idan ba na jin barci, sai in kidaya mutanen dake kauyen, a waccan lokaci ina tsamanin kauyenmu ba shi da makoma."

Ta ya ya za a kyautata zaman rayuwar jama'ar wurin? Daga shekarar 2017, aka fara bullo da wata hanya da ta dace don raya wannan kauye, wato yiwa tsoffin gine-gine gyaran fuska, ko da yake wadannan gine-gine na gargajiya na da salonsu mai ban sha'awa, amma sun gaza samun kyautatuwa. Saboda ganin haka, kauyen ya gabatar da shirin hayar wadannan gine-gine na tsawon shekaru 15, wato hukumar kauyen ta bada hayar wadannan gine-gine ga wasu mutane daga sauran wurare, wadanda suka zama sabbin mambobin kauye kamar Meihong. Wadannan sabbin mambobi kuwa sun zuba jari don yiwa gine-ginen gyaran fuska da kafa harkokinsu da gudanar da rayuwarsu a nan.

Wadannan sabbin kauyawa sun zo ne daga wurare daban-daban na kasar Sin, dukkansu suna sha'awar muhalli mai kyau na wannan wuri, wasu sun gyara gine-gine zuwa dakunan kwana, wasu zuwa dakunan shan kofi, yayin da wasu suka mayar da su zuwa dakunan litattafi da sauransu. Wata daga cikinsu Zen Wanzhen ta ce:  

"Mun zo nan don ba da gudunmawarmu ga wannan kauye. Da kuma yayata al'adu da fasahohin kauyen, ba ma kawai mun samu biyan bukatunmu ba, har da kawo alfanu ga sauran mutane."

Wadannan sabbin kauyawa sun kawowa kauyen sabon salon zaman rayuwa da ma kudade da bunkasuwa. Mazauna wurin sun ganewa idanusu sauye-sauye masu kyau a wurin, sun fara koyon fasahohi daga malamai. Bakauye Chen Xiaozhen ya ce:

"Malami ya nemi mutane 30 don su koyi fasahar zanen mai, daukacinmu ba mu san yadda za a yi amfani da alkalami ba, balle zanen mai."

An gabatar da shirin yadda wadannan kauyawa 30 suka koyi fasahar zanen mai a kan Intanet, abin da ya jawo hankalin masu kallo matuka, matakin da ya baiwa kauyawa kwarin gwiwa. Yanzu kuma, tun daga tsofuwa mai shekaru fiye da 80 a duniya zuwa kananan yara masu shekaru 5 ko 6 a duniya, sun iya zane. Har ma matasa da suka fita waje sun koma kauye don fara wasu harkoki, kuma suna koyon fasahar zane da wasan kwaikwayo da dai sauransu Hakan ya sa, kauyen Longtan ya zama wani tauraro a wannan wuri. A shekarar bara kuma, kauyen ya jawo hankalin masu yawon shakatawa fiye da dubu 200.

Yanzu, an fara yiwa wasu gine-gine na gargajiya gyare-gyare a sabon zagaye don gyara fuskar kauyen ta yadda za a jawo hankalin masu bude ido daga gida da waje. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China