Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abubakar Ayuba Isah: Ci gaban kasar Sin ya burge ni sosai
2020-08-18 14:56:41        cri


Abubakar Ayuba Isah, wani dalibi ne daga jihar Kanon tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na farko a fannin tattalin arziki da kasuwancin kasa da kasa a jami'ar nazarin albarkatun man fetur a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, ko kuma Southwest Petroleum University a turance.

A zantawarsa da Murtala Zhang, Abubakar Ayuba Isah ya bayyana cewa, yana jin dadin zaman rayuwa da karatu a nan kasar Sin, duk da cewa yanayin karatu tsakanin gida Najeriya da kasar Sin ya bambanta kwarai. Abubakar ya kara da cewa, farkon zuwansa kasar Sin, ya gamu da matsalolin abinci, amma yanzu ya saba da abincin kasar sosai.

Abubakar ya kara da cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki da zaman rayuwa ya burge shi kwarai da gaske, abun da ya karfafa masa gwiwar kara neman ilimi domin bautawa kasarsa Najeriya. Ya kuma yi kira ga matasan Najeriya da su maida hankali kan muhimmancin ilimi, saboda a cewar malam Bahaushe, ilimi shi ne hasken rayuwa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China