Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwajin rigakafin COVID-19 na kasar Sin yana samun tagomashi
2020-08-16 16:48:57        cri
Alkaluman sakamakon gwajin alluran rigakafin annobar COVID-19 wanda kasar Sin ta samar yana cikin yanayi mai inganci kuma yana samar da kyakkyawan sakamako, kamar yadda mujallar kiwon lafiya ta Journal of the American Medical Association ta fitar a wannan mako.

Takardar bayanan binciken ta yi tsokaci kan mataki na 1 da na 2 na sakamakon gwajin alluran rigakafin cutar ta COVID-19 wanda cibiyar gwajin kwayoyin halittu ta Wuhan karkashin kamfanin nazarin kimiyyar halittu ta kasar Sin CNBG , da kuma cibiyar nazarin kwayoyin cuta karkashin kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin suka samar.

Binciken ya kunshi bayanan da aka samu daga gwajin da aka yi wa mutane 320 'yan tsakanin shekaru 18 zuwa 59, wadanda suka karbi gwajin bisa son ransu, inda mutane 96 suka shiga aikin gwajin a mataki na 1, kuma mutane 224 suka shiga mataki na 2 na gwajin rigakafin.

Sakamakon ya gwada cewa, rigakafin yana da matukar inganci wajen samar da garkuwar jiki ga mutanen da aka yiwa gwajin rigakafin, karfin da rigakafin ke da shi yana da matukar tasiri wajen baiwa jiki kariya.

Takardar binciken ta nazarci ingancin rigakafin, sakamakon ya gwada cewa, rigakafin bashi da wata illa mai yawa ga jikin dan adam. Abin da kawai yafi zama damuwa shine zafin da za'a ji sashen da aka yi allurar, sai kuma dan zazzabi kadan dake biyo bayan allurar, sai dai dukkansu ba masu wani tasiri na azo a gani bane ga jikin dan adam.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China